
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya miƙa sabon jaddawalin mutane 32 da za a ba su muƙaman jakadanci ga Majalisar Dattawa domin tantancewa da kuma tabbatarwa.
An ruwaito cewa shugaban ƙasar ya yi aiken buƙatar ne a takardu guda biyu zuwa ga Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.
A sanarwar da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya nemi majalisar da ta yi nazarin tabbatarwa akan wasu ƙwararru a fannin guda 15 da waɗanda basu da ƙwarewa su 17 domin wakiltar Nijeriya a manyan ofisoshin jakadancin a ƙasashen duniya.
Sunayen manyan ƴan siyasa da tsofaffin jami’an gwamnati da ba su da ƙwarewa a jaddawalin kamar yadda NewsPointNigeria ta ruwaito, sun haɗa da:
“Barrister Ogbonnaya Kalu (Abia)
Reno Omokri (Delta), author and former presidential aide
Professor Mahmud Yakubu, former INEC chairman
Erelu Angela Adebayo, former First Lady of Ekiti State
Rt. Hon. Ifeanyi Ugwuanyi, former governor of Enugu
Tasiu Musa Maigari, former Katsina Assembly Speaker
Yakubu N. Gambo, former Plateau Commissioner and ex-UBEC deputy executive secretary
Professor Nora Ladi Daduut, former Plateau senator
Otunba Femi Pedro, former Lagos State Deputy Governor
Chief Femi Fani-Kayode, former Aviation Minister
Barr. Nkechi Linda Ufochukwu (Anambra)
Florence Ajimobi, former First Lady of Oyo
Lola Akande, former Lagos Commissioner
Grace Bent, former Adamawa Senator
Victor Okezie Ikpeazu, former Governor of Abia
Senator Jimoh Ibrahim, businessman and senator from Ondo
Ambassador Paul Oga Adikwu, former envoy to the Vatican”
Sai kuma waɗanda ke da ƙwarewa a fannin, waɗanda suka haɗa da:
“Enebechi Monica Okwuchukwu (Abia), Yakubu Nyaku Danladi (Taraba), Miamuna Ibrahim Besto (Adamawa), Musa Musa Abubakar (Kebbi), Syndoph Paebi Endoni (Bayelsa), Chima Geoffrey Lioma David (Ebonyi), Mopelola Adeola-Ibrahim (Ogun), Abimbola Samuel Reuben (Ondo), Yvonne Ehinosen Odumah (Edo), Hamza Mohammed Salau (Niger), Ambassador Shehu Barde (Katsina), Ambassador Ahmed Mohammed Monguno (Borno), Ambassador Muhammad Saidu Dahiru (Kaduna), Ambassador Olatunji Ahmed Sulu Gambari (Kwara), and Ambassador Wahab Adekola Akande (Osun)”, kamar yadda ta wallafa.
A cewar Onanuga, za a ƙara fitar da jaddawalin ƙarin wasu sababbin jakadun nan ba da jimawa ba yayin da Nijeriya ke ƙoƙarin ƙarfafa harkokin difulomasiyyarta a sassan duniya.
