Yaƙi da ƙwaƙwalwa

Spread the love

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ

Ba fa a banza Allah ya yi kiran a yi amfani da kwakwalwa, wato a rika tunani, nazari, bincike, duba, kallo (tadabburi iri-iri) a wurare sama da 800 cikin Qurani ba. Umarnin da ya zarta kowane irin umarni hatta na sallah da zakka da aikin hajji. Dalili shine amfani da kwakwalwar da Allah ya huwace mana shine ya banbanta mu da duk sauran halittu a duniya, kuma abinda ke tabbatar da Imani wajen banbance gaskiya da bata, ci gaba da koma baya, nasara ko akasinta.

Ba a harkokin Imani kadai ba, hatta a harkar yau da kullum ko tsarin rayuwa, duk al’ummar da ta rungumi amfani da kwakwalwar ta fiye da sauran al’ummar zamaninta, tsawon tarihi zaka samu ita ce jagorar zamaninta.

Kamar yadda a yanzu, Turawa, wadanda kwaikwayon wannan dabi’ar daga musulmi a baya ita ta kai su tsaikon da su ka kasance a yanzu, kuma a gaban mu muna ganin yadda China ke kokawar kwace musu wannan matsayin sakamakon dabbaka wannan tsarin.

Ta kowacce fuska a tsawon shekaru 300-400, Turawan yamma sun yake mu da basira wajen tabbatar da cewa mun mika wuya ga jagorancinsu ta hanyar danne tunaninmu. Hatta addini, sun bi hanyoyin tabbatar da cewa ba mu dabbaka kyawawan koyarwarsa ba sai amfani da shi a gurgunce.

Idan aka kalli wannan taswirar ta Duniya, ita kadai ce irinta, wadda ta fitar da fadin kasa na kowacce nahiya a hakikanin yadda su ke a zahiri. Duk sauran taswirori da zaka ci karo dasu zaka samu cewa nahiyar Turai da Amurka sun fi kowa fadin kasa, Alhãli kuwa nahiyar Afirka za ta iya daukar Amurka, Russia, India da Brazil. Amma Greenland, wato nahiyar kankara ta Arewa-maso-yammamacin Turai za ku ga ta kusa girman Afirka ita kadai, alhãli ba ta fi girman Democratic Republic of Congo ba.

Wannan ya samo asali tun daga Karni na 16th lokacin British Empire da colonization na turawa. Shahararren cartography, mai zanen taswira, Mercator ya zana taswirar Duniya domin tallafawa turawa a yunkurin su na mamayar Duniya da nuna cewa sun fi kowa fadin kasa (projection of power). Hakan yayi tasiri tsawon shekaru 400. Amma sakamakon sun cimma burinsu na wancan lokacin, yanzu sun dawo su na canza waccan taswira da wannan a makarantun domin baiwa Yayansu, Ilimi na hakika ba na yaudara ba.Ka ga laifinsu? Ita kwakwalwa Allah ya bamu ita domin yin tunani domin saduwa da ilimi, wanda ko dai ka yi yadda zai kawo alheri ko kuma sharri. Allah ya Dade da kalubalantar mu cewa… Q30:8 “Shin, ba sa yin tunãni a cikin zukãtansu?” Ko kuwa wannan cajin ne ya hau kanmu? Q47:24 “Shin to, bã sa tunani ne game da Alƙur’ãni, kõ kuwa a kan zukãtansu akwai makullai ne?”

By ukarofi