Gwamnonin Nijeriya shida da suka taɓa zaman kurkuku a Nijeriya

Spread the love

Cin hanci da rashawa na daga manyan ƙalubalen da suka addabi Najeriya tun bayan dawowa tsarin dimokuraɗiyya a 1999. A 2012, an kiyasta cewa ƙasar ta yi asarar sama da dala biliyan 400 tun bayan samun ‘yancin kai.

A bisa rahoton Transparency International na 2024, Najeriya ta samu maki 26 cikin 100 a jerin Corruption Perceptions Indeɗ (CPI) — ɗan ɗigogi sama daga maki 25 da ta samu a 2023. Har yanzu an saka ta a matsayin ƙasa ta 140 cikin ƙasashe 180, lamarin da ke nuna matuƙar yawaitar cin hanci a sashen gwamnati.

Ko da yake an samu ɗan ƙaramin cigaba, maki da Najeriya ke samu bai kai matsakaicin maki na duniya (43) ba — alamar cewa har yanzu ƙalubale irin su rigakafin cin hanci, gaskiya, da bayyana ayyukan gwamnati na nan daram.

A ƙididdigar hukumomi, zuwa yanzu tsoffin gwamnoni shida ne aka yanke wa hukunci kan manyan laifukan rashawa da makamantansu.

Matsalar cin hanci bata tsaya kan ma’aikatan gwamnati ba kawai ta ratsaya kowane ɓangare, wato masu muƙamai na siyasa, wanda a can ɗin ne abin ya fi ƙamari.

Duk da ana ganin kamar manyan ‘yan siyasa sun fi ƙarfin a hukunta su, amma hakan bai hana shigar wasu daga cikinsu gidan gyaran hali ba. 

A yau za mu yi duba ne kan jerin gwamnoni shida da suka samu kansu a gidan gyaran hali;

1. Lucky Igbenedion:

Lucky Igbenedion, tsohon gwamnan Jihar Edo (1999–2007), shi ne gwamna na farko a tarihin Najeriya da aka tuhume shi aka kuma same shi da laifin karkatar da kuɗaɗen jama’a.

Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ta gurfanar da shi da zarge-zarge 142, ciki har da karkatar da aƙalla dala miliyan 24 ta hanyar boge.

A 2008, ya shiga yarjejeniyar ‘plea bargain’ (wata yarjejeniya da shari’a ta halasta, inda mai laifi bayan ya amsa laifin wawusar kuɗaɗen jama’a zai dawo da wani kaso na kuɗin sai a yafe masa saura) wanda ya ba shi damar mayar da wani ɓangare kacal na abin da aka zarge shi da satar, lamarin da ya sa aka saki gwamnan.

2. Marigayi Diepreye Alamieyeseigha:

Marigayi Diepreye Alamieyeseigha ya yi mulki a Jihar Bayelsa (1999–2005). A 2007, an yanke masa hukuncin shekara biyu a gidan yari bisa laifukan rashawa da kwashe kuɗi. Kafin wannan hukunci, ya shafe kusan shekaru biyu yana tsare yayin jiran shari’a.

A 2005 an kama shi a Landan, inda aka ce ya tsere ya koma Najeriya da rigar mata don kauce wa hukunci. Daga ƙarshe aka tsige shi daga kujerarsa, sannan aka soma kwace wasu ƙadarorin da yake da su a Birtaniya.

A ranar 10 ga Oktoba 2025, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Port Harcourt sakamakon bugun zuciya.

3. Joshua Dariye:

Joshua Chibi Dariye, tsohon gwamnan Filato kuma tsohon sanata, ya yi fice a jerin shari’o’i mafi tsawo da suka ja hankalin duniya.

A Janairu 2004, jami’an Metropolitan Police na Birtaniya suka kama shi kan zargin wanke kuɗi. Sun gano maƙudan kuɗaɗe da suka danganta da karkatar da kusan dala miliyan 9 na kuɗaɗen gwamnati.

A 2007 EFCC ta gurfanar da shi da zarge-zarge 23, ciki har da karkatar da Naira biliyan 1.126 na kuɗin muhalli na jihar.

A 2018, Babbar Kotun Abuja ta same shi da laifin zamba cikin aminci da karkatar da Naira biliyan 1.6. Alƙaliyar, Justice Adebukola Banjoko, ta yanke masa shekara 14, daga baya kotun ɗaukaka ƙara ta rage zuwa shekara 10.

A cikin 2022, ya samu afuwar shugaban ƙasa, ko da yake shari’arsa ta kasance darasi kan gasar gwamnati da rashawa.

4. James Ibori:

James Onanefe Ibori, tsohon gwamnan Delta kuma ɗaya daga manyan ‘yan siyasar yankin, ya fafata da shari’a ɗaya daga cikin mafi girma a tarihin Najeriya da Birtaniya.

A 2012, kotun Southwark Crown Court ta yankewa Ibori shekara 13, bayan ya amsa laifuka goma da suka shafi wanke kuɗi da zamba.

An bayyana cewa ya karkatar da aƙalla dala miliyan 250 daga kuɗin Jihar Delta. Rahotanni sun ambaci ƙadarori masu daraja, motoci, gidaje da asusun wajen ƙasa da aka cika da kuɗin jama’a.

A ƙarshe ya yi kusan shekara huɗu kacal a kurkuku, inda lokacin da ya shafe a tsare da dokar sakin wuri suka rage masa. A 2016 aka sake shi, ya koma gida Najeriya, kuma har yanzu yana da tasiri a siyasar Jihar Delta.

5. James Bala Ngilari:

James Bala Ngilari ya yi mulki a Jihar Adamawa na tsawon watanni bakwai kacal a 2015.

A 2016, EFCC ta same shi da laifin ba da kwangilar sayen motocin Naira miliyan 167 ba tare da bin ƙa’ida ba. Kotun ta yanke masa shekara biyar ba tare da zaɓin biyan tara ba.

Sai dai daga baya kotun ɗaukaka ƙara ta wanke shi, ta ce an yi kuskuren shari’a a matakin farko.

6. Orji Uzor Kalu:

Senator Orji Uzor Kalu, wanda ya yi mulki a Abia (1999–2007), shi ma ya fuskanci babbar shari’a kan almundahanar kuɗi.

A 2019, kotun tarayya ta Lagos ta same shi da laifuka 27, ciki har da karkatar da Naira biliyan 7.65. Alƙalin da ya yi shari’ar, Justice Mohammed Idris, ya yanke masa shekara 12, yayin da kamfaninsa SLok da wani jami’insa ma aka same su da laifi.

Amma a 2020, Kotun Koli ta rushe hukuncin gaba ɗaya, tana cewa kuskuren tsarin shari’a aka yi, lamarin da ya sa aka sake shi daga gidan yari.

Abin tambayar a nan dai shi ne, ko akwai gwamnonin da ke kan mulki yanzu da ake ganin za su iya shiga irin wannan jerin nan gaba?

By ukarofi