Kanu: Ƙarshen tika-tika-tik

Spread the love

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Shari’ar da a ka fara ta tun 2015 ta samu ayyanennen hukunci na farko bayan dambarwar kai kawo har ma da yanda shugaban na ‘yan awaren Biyafara na IPOB Nnamdi Kanu ya taba arcewa bayan samun beli da hakan ya jefa wanda ya tsaya ma sa Sanata Abaribe shiga tsaka mai wuya. Bayan kamo Kanu daga Kenya a 2021 an koma shari’a kuma Kanu ya buƙaci lallai sai an sauya ma sa Jostis Binta Nyako da ita ce asalin mai yi ma sa shari’a.

A tsarin dokokin Nijeriya wanda a ke tuhuma ba mai laifi ba ne sai kotu ta yanke ma sa hukunci da samun sa da laifi. Karshe dai babbar kotun tarayya ta yankewa madugun ‘yan awaren Biyafara na IPOB Nnamdi Kanu hukuncin daurin rai da rai. Yanzu dai ya nuna Kanu ya zama mai laifin ta’addanci kuma ya ma samu sassauci don alƙalin ya duba aya ta 23 a sura ta 23 a littafin Matta cikin Sabon Alkawari Linjila da ke buƙatar sassauci ko mutunta rai. Alƙali James Omotosho ya ce a maimakon hukuncin kisa bisa laifin Nnamdi Kanu na haddasa kashe mutane da daman gaske ciki da ɗimbin sojoji da ‘yan sanda da Hausawa da sauran ‘yan Arewa; ya rage zafin hukuncin zuwa daurin rai da rai. Omotosho ya ce a duk lokacin shari’ar Kanu, ya lura shugaban na tawaye bai nuna nadama ba, ga girman kai rawanin tsiya. Kanu kan tashi a gaban kotun ya yiwa kowa wankin babban bargo har ma ya ayyana korar lauyoyinsa. Gangancin da ya yi shi ne kotu ba galala ba ce kamar ‘yan amshin shatansa na Kudu da Arewa. Haƙiƙa hayaniyar Kanu ba za ta tsorita kotu ta ki yin aikinta ba bisa doka. Akwai alamun da Omotosho ya nuna inda Kanu ya yi nadama ba mamaki a yanke ma sa hukuncin wasu ‘yan shekaru daga bisani ma gwamnati ta iya yafe ma sa. Bakaken maganganu irin na jagoran magoya bayansa na Arewa Ouba Ali Mohaman daga Kamaru; ya ja ma sa hukuncin na dauri duk da ma alkali bai fusata da rashin ɗa’a ta Kanu ba, ya yi ma sa sassauci.

Daya daga tsoffin lauyoyin Kanu, Aloy Ejimakor ya yi caraf ya ce za su ɗaukaka ƙara. Wannan dai hurumin kotu ne har zuwa kotun koli wajen bitar hukuncin. Don wani ya aikata laifi kuma ba a kai ga cafke shi ba, ba shi ke nuna wanda ke hannu ba shi da laifi ba. Mu na amfani da wannan dama wajen yaba wa jami’an tsaro da yanda su ka murƙushe dimbin ‘yan ta’adda a kowane sashe na Nijeriya inda daga 2023 a ka kashe fiye da ‘yan ta’adda 13,000. Kun ga dubban nan da a ka kashe ai tasu ta kare sai kuma a gaban mahalicci; waɗanda ba su shigo hannu ba kuma dubunsu zai cika da yardar Allah.

Don haka masu yayata lallai a saki Nnamdi Kanu su shafawa kan su ruwa don duk mai irin wannan ya na cikin idon mikiya na jami’an tsaro kuma za a iya cafke shi koyaushe a gurfanar da shi gaban kotu don zama da hannu a lamuran ruruta ta’addanci a Nijeriya.

’Yan IPOH wato wasu da ke iƙirarin al’ummar asali mazauna ƙasar Hausa duk da farafagandar ruruta fitinar ƙabilanci ce masu marawa IPOB baya su shiga taitayinsu don da na gaba a ke gane zurfin ruwa. Duk baƙar zuciyar mutum ya riƙa takatsantsan da dokokin kasa, don kuwa inda barazana da fushi za su haifawa wani da a ke tuhuma alheri, da kotu ta ji tsoron Nnamdi Kanu mai dukan teburin kotu ya furta duk abun da ya ga dama.

Da sauƙi ga waɗanda ka iya bijirewa don rashin kishin ƙasa wajen shirya zanga-zanga a ƙetare kan Kanu. Idan wani ya shigo Abuja da zummar irin wannan zanga-zangar zai yaba wa aya zaƙi. Ba kasa mai ‘yanci da za ta zuba ido wani mutum dan tawaye ya yi ta ingiza mutane don a wargaza ƙasar har ma da zayyana kasa mai ‘yanci a matsayin gidan ajiyar dabbobi. Gaskiyar magana jami’an tsaro sun yi namijin ƙoƙari wajen amfani da bayanan sirri da su ka kai ga cafko Kanu da ingizo keyarsa gida daga kasar Kenya a 2021. In mutum zai yi sara ya riƙa duba bakin gatari.

Babu Gagarerre sai Barerre:

ɗan ta’adda Kanu ya dauka Jostis Omotosho zai ji tsoronsa ne ya sake shi, shi ya sa ya rika tada hayaniya a kotu, ya na dukan tebur da furta bakaken kalamai na cin mutunci ga masu shari’a da ma sashen shari’ar. Can waje kuma ga wasu ‘yan ta zubar da ba sa ƙaunar haɗin kan Nijeriya na gudanar da zanga-zanga da buƙatar lallai sai a sake Kanu. Shin tunzurin da su ke yi ga kotu ne ko fadar shugaban ƙasa? Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zo ya samu wannan shari’a na gudana kuma ga bayanai na sanadiyyar kashe mutane da daman gaske ciki da jami’an tsaro da a ke tuhumar Kanu. Kawai don matsin lamba daga wasu ‘yan son zuciya kurum shugaban ƙasa ya ce a sake shi ya yafe ma sa. Haba ai gwamnati ba wasa ba ne kuma ko waɗanda a ke yi wa ahuwa za ka ga sai sun zauna a gidan yari na wani lokaci kafin a yi bitar laifin da su ka aikata. Akwai Maryam Sanda da laifin da ta aikata shi ne kashe mijinta Bilyaminu Bello wanda a nan rai ɗaya ne. In mun duba ‘yan IPOB yaran Kanu sun kashe wata mata ‘yar asalin jihar Adamawa da ‘ya’yanta kakaf. Kazalika akwai wata mata soja ta tafi da abokin aikinta soja don ganawa da ‘yan uwa a kudu maso gabar kan shirin aure, haka miyagun nan su ka kashe su da yagalgala namansu! Muguntar ta Kanu fa ta wuce hankali.

Laifin Kanu da ya fi muni shi ne farfaɗo da rigimar da ta haddasa yaƙin basasar Nijeriya daga 1967 rayuka da dama su ka salwanta. Madugun ‘yan awaren Biyafara Odumegwu Ojukwu ya arce ƙasar Ghana har sai lokacin da marigayi tsohon shugaba Shagari ya yafe ma sa ya dawo kuma ya shawarci mutanensa da su dakata da wannan tunanin hakanan “na jagoranci ballewa ta kafa Biyafara kuma ina alfahari da haka, amma ba na ganin sake maimaita haka ya na da amfani” Inji Ojukwu. Sai a ka samu wani sabon dan tawaye na zuga mutane su dau makamai su yi ta kisa kawai su zubar da jini ba abun da za a yi. Bai ma tsaya a nan ba sai da ya yi ta furta miyagun kalmomi na raina Nijeriya a idon duniya. Rashin hangen nesa ya sa ya ɗauka don ya buya a Birtaniya shikenan ba za a iya kama shi ba. A nan mu na kara jinjinawa jami’an tsaron Nijeriya da su ka ingizo keyar Kanu daga Kenya don fuskantar shari’a. A nan ina gargadin uban ‘yan kwangilar rusa Arewa Ouba Ali Mohaman na Kamaru cewa ya kara shiga taitayinsa don kasancewar sa dan Kamaru ba zai gujewa cafkewa da gurfanarwa gaban kotu ba. Wuta da ya ke cillowa Nijeriya da yayyafa ruwa a Kamaru ba zai ɗore da lamunta da hakan ba. Haƙiƙa za a wayi gari a samu hukumar da za ta miƙo shi Nijeriya don ya girbi muguntar da ya shuka. Allah zai yi maganinsa tun da mugun mutun ne mai cike da guba da shaidanci.

Ga sauran ‘yan ta’adda su jira lokaci ne duk wanda a ka cafke zai yabawa aya zaki. Ko Abubakar Shekau da ya buya a dajin Sambisa bai kai labari ba, don hikimomi da addu’o’i sun sa jama’arsa sun ɗau mataki a kan sa. Ga Buharin daji mun san labarin yanda Dogo Gide ya sheke shi. Misalan ma su na da yawan gaske. Duk wanda ka ga ya na cigaba da ta’addanci kamar ba zai shiga komar hukuma ba, ba shi da hankali don haƙiƙa makashin maza, maza kan kar shi. Janar Zamani Lekwot ne ya tsallake rijiya da baya duk da an samu hannusa dumu-dumu a fitinar Zangon Kataf da ta lakume rayukan maza, mata da ƙananan yara har ma masu juna biyu; a ka yanke ma sa hukuncin kisa, amma gwamnatin soja a 1995 ta rage hukuncin zuwa ɗaurin wani dan lokaci a ka sake shi. Mu sani ko an yafewa mutum laifi a duniya akwai wata shari’ar a gobe kiyama. In Allah ya yarda za mu yi bitar abun da ya faru a Zangon Kataf.

Kammalawa:

A halin yanzu, bisa labarai na kafafen labarai, mun ji an kai Kanu gidan yari a Sokoto, don fara zaman ɗaurin rai-da-rai. Kazalika za a jira niyyar ɗaukaka ƙara daga muƙarraban Kanu kamar yadda tsohon lauyansa Ejimakor ya bayyana. Son samu duk ‘yan ƙasa nagari su mutunta hukuncin kotu kuma in wani hukunci bai mu su daɗi ba, su na da zaɓin ɗaukaka ƙara har zuwa kotun ƙarshe ta Allah ya isa. Barazana ga gwamnati kan za ta rasa goyon baya a kudu maso gabar kan wannan hukunci mummunar ajanda ce ta maƙiya Nijeriya waɗanda ba su damu da wargajewar ƙasar ba don dalilai na son zuciya. Matuƙar za mu zauna tare a Nijeriya sai mun mutunta dokokin ƙasa sau da kafa. Duk wata barazana ga gwamnati ko kotu ba wani tasirin da za ta yi saboda haƙiƙanin lamari duk mai yaƙi da hukuma shi zai sha ƙasa ya kuma zama abun tausayi.

By ukarofi