Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Salisu Masu, ya bayyana cewa burinsa shi ne idan Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya samu damar yin wa’adi na biyu ya kammala shekaru takwas a kan mulki, mataimakinsa, Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya gaje shi a matsayin Gwamnan Kano.
Hon. Masu ya ce wannan ra’ayi nasa ya samo asali ne daga ganin cewa Gwarzo mutum ne mai gogewa, jajircewa, da kuma cikakkiyar fahimtar akidar madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso. Ya bayyana haka ne a wajen taron raba tallafin jari ga mata 200 na ƙaramar hukumar, wanda aka gudanar a harabar ofishin ƙaramar Hukumar Fagge a makon da ya gabata, inda Hon. Nasiru Garba Kunya, mai bai wa Gwamnan Kano shawara kan harkokin ƙungiyoyi, ya wakilci Gwamna Abba a wurin.
Shugaban ƙaramar hukumar ya yi kira ga dukkan matan da suka karɓi tallafin N50,000 su yi amfani da shi yadda ya dace wajen bunƙasa sana’arsu domin kula da iyalansu da ‘yan uwa, tare da tabbatar da cewa manufar gwamnatin Kano ita ce karfafa mata wajen dogaro da kai.
A ƙarshe, Hon. Salisu Masu ya yaba wa Gwamnan Kano, mataimakinsa, da sauran jami’an gwamnati kan jajircewar da suke yi wajen ci gaban Kano—musamman a fannonin ilimi, lafiya, hanyoyi, sufuri, da sauran muhimman abubuwan more rayuwa. Ya yi kira ga al’ummar Kano su ci gaba da ba gwamnati goyon baya ta hanyar addu’a domin samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, da wadatar arziki a Kano da Nijeriya baki ɗaya.
