
Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa kuma iyalinka marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, ta bayyana wani lamari mai tayar da hankali da ya faru a lokacin mulkin marigayin inda ta ce a wani ɗan lokaci Buhari ya yarda da jita-jitar da ake yaɗawa a Fadar Shugaban Ƙasa cewa ita ce ke shirin sanya masa guba ko ƙoƙarin halaka shi.
Wannan bayani ya fito ne a cikin wani sabon littafin tarihin Buhari mai shafuka 600, mai taken ‘From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari’, wanda Dr. Charles Omole ya rubuta, kuma aka ƙaddamar da shi a ranar Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
A cewar littafin, Aisha Buhari ta ce jita-jitar da aka yaɗa a cikin fadar ta sa tsohon shugaban ƙasar ya shiga fargaba na ɗan lokaci, har ta kai ga kulle kansa a ɗaki, tare da sauya wasu muhimman al’adu na rayuwarsa ta yau da kullum.
“Sai jita-jita da tsoratarwa suka fara. Aka ce ina shirin kashe shi,” in ji Aisha Buhari kamar yadda littafin ya ruwaito.
Ta bayyana cewa Buhari ya yarda da wannan labari na tsawon kusan mako guda, lamarin da ya sa ya fara kulle ɗakinsa, ya sauya halayensa, kuma mafi muni—aka rikice da tsarin abincinsa da magungunan kari (supplements).
Aisha Buhari ta jaddada cewa matsananciyar rashin lafiyar da Buhari ya shiga a shekarar 2017, wadda ta kai shi hutun jinya na kwanaki 154 a Birtaniya, ba guba ba ce, kuma ba wata cuta mai ban tsoro ba, illa dai tangardar abinci da dakatar da magungunan kari da take kula da su da kanta tsawon shekaru.
“Shekara guda bai cin abincin rana ba. An lalata masa tsarin cin abinci,” inji ta.
Ta ce, da zarar an dawo da tsarin abinci da magungunan kari yadda ya dace a Landan, lafiyar Buhari ta farfaɗo cikin gaggawa, har ya yar da sandar tafiya bayan kwana uku kacal.
Littafin ya kuma taɓo matsalolin rashin yarda da juna a cikin fadar shugaban ƙasa, ciki har da zargin sa ido kan juna, da kuma ƙaryata shahararriyar jita-jitar “Jibril of Sudan”, wadda ta yi ta yawo a kafafen sada zumunta.
