Hukumar NFC a shirye take ta bada goyon baya ga masu harkar fim – Ali Nuhu 

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU 

Shugaban Hukumar kula da bunƙasa harkokin fim ta Nigerian Film Corporation’ Ali Nuhu, ya bayyana ƙudirin hukumar na bada goyon bayanta ga dukan ayyukan da suka shafi harkar fim a ƙasar nan.

Ali Nuhu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron horar da marubutan labarin fim da aka gudanar a ranar Asabar ɗin da ta gabata a ɗakin taro na Kannywood TV dake titin Muhammadu Buhari a cikin garin Kano.

Tun da farko ya bayyana muhimmancin rubutun labari wanda ya kasance kashin bayan duk wani fim da za a shirya. Inda yake cewa “Kashin bayan kowanne fim labari ne, idan labarin bai rubutu ba, to akwai matsala babba.. domin akwai fina-finan da idan aka kalle su za ka ga cewa ba wani abu ba ne ya ja hankalin mutane illa kamar yadda aka rubuta labarin. Ko kuma a ce maka yadda marubucin ya rubuta jarumin fim ɗin, ko kuma a ce salon maganar da aka yi amfani da shi a fim ɗin da dai yadda aka tsara rubutun labarin. Don haka muna jinjina ga marubuta gaba ɗaya.”

Haka kuma a cikin bayanin nasa shugaban hukumar Ali Nuhu ya kuma bayyana cewa ” Anan abin da nake so na faɗa ita Hukumar mu ta bunƙasa harkokin fim ta ƙasa a koda yaushe a shirye take ta bada goyon baya da kowanne fanni na aikin fim, walau jarumai ne masu ɗaukar shi ne da duk wani ɓangare na harkar fim, idan suka kawo wata fasahar su na wani abu da suke so su yi domin su taimaki masana’antar  yadda za ta ci gaba, to za mu bada goyon baya.”

Haka nan ya yi kira ga marubutan da su mayar da hankali wajen rubuta labarin ban dariya wanda a yanzu shi ne masu kallon fina-finai suka fi buƙatar kallo, kuma fina-finan ban dariya su ne suka fi kawo kuɗi a cikin finafinan da ake shiryawa.

By ukarofi