
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Alamu sun bayyana cewa sauran ɗaliban makarantar St. Mary’s Catholic School, Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Rafi ta Jihar Neja sun shaƙi iskar ƴanci bayan shafe tsawon makonni a komar ƴan bindigar da suka yi awon-gaba da su.
Hakan na zuwa ne bayan da iyayen yaran suka koka wa gwamnatocin tarayya da ta jihar akan a yi ƙoƙarin ceto yaran gabanin bikin Kirsimeti.
Zuwa yanzu dai sauran ɗalibai guda 130 na makarantar da ke hannun ƴan bindiga sun kuɓuta, inda jimillar adadinsu ya kai 230.
Yanzu dai za a iya cewa babu sauran ɗaliban makarantar Papiri ko ɗaya da ke hannun ƴan bindiga.
A lokacin da maharan suka yi garkuwa da ƴan makarantar, sun shafe aƙalla sa’o’i uku suna atisaye, inda daga nan suka tafi da su cikin dazukan da ke kusa da yankin.
