Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Tarayya ta bada hutun Kirsimeti da na sabuwar shekara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun 25 da 26 ga watan Disambar 2025 da kuma 1 ga watan Junairun 2026 a matsayin lokacin hutun bikin Kirsimeti, ranar boksin da kuma murnar shiga sabuwar shekara.

Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Dakta Magdalene Ajani ta bayyana haka a wata takarda, yau Litinin.

Ta ce, Ministan ma’aikatar, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya sanar da haka a madadin Gwamnatin Tarayyar.

Ya yi kira ga al’umma da su yi amfani da lokacin wajen ƙarfafa soyayya, zaman lafiya, tausayi da sadaukarwa a tsakaninsu yayin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa (AS).

Tunji-Ojo ya kuma kirayi ƴan Nijeriya daga kowane addini ko ƙabila da su yi amfani da lokacin wajen yi wa ƙasar addu’o’in samun zaman lafiya, tsaro da ci-gaba.

Haka kuma, ministan ya roƙi ƴan ƙasa da su cigaba da kasancewa masu ƙoƙarin kiyaye doka da oda da sanya ido akan lamuran da suka shafi tsaro a yayin bukukuwan.

By Babaji