Zakka da waƙafi na taimakawa wajen rage kyashi, hassada da talauci – Dikko Radda

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar tawagar gamayyar ƙungiyoyin Zakka da Waƙafi na Najeriya (AZAWON), wadda ta kawo masa ziyarar aiki a fadar gwamnatin jihar.

Ya jaddada cewa Zakka da Waƙafi ba wai kawai ibada ba ce, illa wata muhimmiyar hanya ta rage raɗaɗin talauci, ƙarfafa jin ƙai, tsaftace zuciya, da samar da adalci a cikin al’umma.

A cewarsa, yadda ake tara da rarraba zakka cikin tsari yana taimakawa wajen inganta tsaro, domin yana rage yawan matasa marasa aikin yi, tare da samar da damar dogaro da kai ta hanyar tallafawa ƙananan sana’o’i da ayyukan raya alumma.

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Katsina ta ɗauki matakai masu muhimmanci wajen ƙarfafa hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Katsina, ta hanyar inganta tsarin karɓa da rarraba zakka, ƙara gaskiya da riƙon amana, da kuma tabbatar da cewa taimako ga waɗanda suka fi buƙata a kan lokaci.

Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bai wa hukumar cikakken goyon baya domin ta ƙara faɗaɗa ayyukanta a faɗin jihar.

A nasa jawabin, shugaban hukumar zakka da waƙafi ta Jihar Katsina, Malam Ahmad Filin Samji, ya gabatar da rahoton nasarorin da hukumar ta samu a cikin ƙanƙanin lokaci, tare da bayyana shirye-shiryen da aka tanada domin ƙara inganta tsarin zakka da waƙafi da faɗaɗa amfanin da al’umma ke samu daga shirin.

Shima shugaban gamayyar ƙungiyoyin zakka da waƙafi na ƙasa (AZAWON), Sadaukin Sokoto, Engr. Muhammad Lawal Maidoki, ya yabawa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa jajircewarsa wajen tallafawa harkokin addini, musamman ƙoƙarinsa na inganta shirin zakka da waƙafi a Jihar Katsina. Ya kuma tabbatar wa gwamnan cewa AZAWON za ta ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnatin jihar domin cimma ƙarin nasarori masu ɗorewa.

AZAWON ta gudanar da taron ta karo na biyar, wanda ya gudana a ɗakin taro na Hillside a Katsina.

Taron ya gudana ne bisa haɗin gwiwar hukumar zakka da waƙafi ta Jihar Katsina da AZAWON.

Inda masana, shugabanni, da sauran masu ruwa da tsaki suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi inganta shirin zakka da waƙafi, da yadda za a yi amfani da kuɗaɗen zamantakewar Musulunci wajen bunƙasa tattalin arziki, rage talauci, da samar da ci gaba mai haɗa kowa a faɗin Najeriya.

By ukarofi