Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wasu gungun ‘yan ta’addan daji ɗauke da miyagun makamai sun yi dirar mikiya garin Maru ta jihar Zamfara.
Rahotanni sun bayyana cewar ‘yan ta’addan sun kashe mutane uku sun raunata mutane biyar tare da garkuwa da mutum takwas a yayin harin.
Majiyar mu ta tabbatar da cewar, maharan sun shiga garin kimanin karfe biyu na daren jiya.
Wannan harin ba shine Karo na farko ba, majiyar mu ta tabbatar da cewar cikin watanni uku, sun shiga garin kusan sau huɗu.
Ƙaramar hukumar Maru na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi da suka fi fuskantatar matsalar rashin tsaro a faɗin Jihar Zamfara.
Wani mazaunin yankin Muhammadu Usman ya tabbatar wa wakilin mu cewar garin na Maru na cikin mummunan yanayin tashin hankali a halin yanzu.
Yayi Kira ga hukumomi musamman gwamnatin tarayya da ta Jihar Zamfara da su kawo masu ɗaukin gaggawa don ceton alummar yankin daga hannun ‘yan ta’adda.
