Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙaramar hukumar Katsina ta samar da cibiyar da ta gina a cikin makarantar firamare na Muhammadu Dodo a garin Katsina.
Da yake jawabi wajan bikin buɗe cibiyar, shugaban ƙaramar hukumar Katsina Ishaq Miƙidad ya bayyana cewa zai taimaka wa yara maza da mata wajan samun ilimi na zamani.
“Yawancin makarantun boko a kasar nan sun tashi daga rubuce rubuce a takarda zuwa amfani da na’urar kumfuta domin haka dole mu taimakawa yaran mu kada bar su a baya,”Inji Miƙidad.
Miƙidad ya bayyana shirin ƙaramar hukumar na haɗin gwiwa da hukumar jarabawa ta ƙasa JAMB domin cibiyar ta zama ɗaya daga cikin da za a rinƙa gudanar da jarabawar JAMB.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce ya zama dole a samar da cibiyar duba da cewa daga yanzu ɗalibai da za su zauna wa jarabawar NECO da WAEC zasu gudanar ta amfani da kumfuta a duk faɗin ƙasar.
Ya ce tunda gwamna Dikko Raɗɗa ya na sakan masu kuɗaɗen su, ya yi kira ga takwarorin sa da suyi koyi da ƙaramar hukumar Katsina wajen samar da irin wannan cibiya domin zamanantar da harkar ilimi a karkara.
“Abu ne mai kyau ƙananan hukumomin jahar ke ta bada tallafi na kayayyaki, amma ya kamata su koma wajen samar da ilimi ta amfani da na’urorin zamani da zai samar da daidaito da sauran jihohin kasar,”inji Miƙidad.
Da yake ƙaddamar da cibiyar, Gwamna Dikko Raɗɗa ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar bisa hangen nisa da yayi wajen gina wannan muhimmin cibiya.
Ya ce yanzu duniya komai na tafe da zamani, domin haka jihar Katsina ba za a bar ta a baya ba wajen zamanantar da bama harkar ilimi ba ,hatta ma sauran hidimar gwamnati zai koma ta yanar gizo.
Ba a daɗe ba da gwamnatin jihar ta shirya horas da malaman makarantun firamare da na Sakandare akan yadda zasu iya sarrafa kumfuta.
Haka manyan ma’aikatun jihar ta shirya basu horo kan sanin yadda zasu sarrafa na’urar kumfuta,manufa a nan shine nan bada jimawa ba harkokin tafiyar da gwamnatin jihar zai koma a na’urar kumfuta.
