Daga ALI ABUBAKAR SADIQ
Cikin Suratul Waqi’a sai Allah ya tambaye mu cewa; Q56:58-59 “Shin kun ga abinda kuke fitarwa na maniyyi? Shin ku kuke halitta shi ko mu ne masu halittawa.”
Wato Allah ya ja hankalinmu da mu yi nazarin maniyyi domin gano asalin yadda mu ka faro da kuma gwanintar halittarsa. Da farko dai idan bayan namiji ya sadu da mace ya dura mata maniyyinsa, to a cikin maniyyin akwai kwayoyin Mani kimanin miliyan 75 a duk yawan Mani da zai kai cikin cokali guda, wato 5 milliliters kenan.
Kowane daya cikin wadannan kwayoyin maniyyi idan ya sami damar barbarar Kwan mace a mahaifa (fertilization) zai iya zama mutum. Wato angwaye miliyan 75 ne zasu shiga gasar samun amarya guda daya (Kwan mace). A yanayi irin na teku, wadannan kwayoyin Mani miliyan 75 za su fara iyo da tsere domin isa ga inda waccan amarya ke jiran sabon angonta. Allah ya siffanta kwayoyin Mani tamkar yayan kwadi, wato talibanban, yadda su ke da wani katon kewayyen kai da kuma jela, siffar da ke taimaka musu waje iyo a wannan tsere.
Da zarar sun isa ga inda amarya ke dakonsu, kuma wani ikon Allah, Kwan mace shine kwayar halitta (cell) mafi girma a duk cikin kwayoyin halitta na jikin Dan Adam. Don haka dandazon angwayen sai su fara kici-kici a ga wanda tsakaninsu zai sami nasarar fasa Kwan ya shiga ciki. A nan ne wancan design na katon kai da Allah ya basu ke tasiri wajen gware a jikin Kwan. Sannan wannan katon kan na dauke da sinadarin halittar gado (chromosomes) 23, wato rabin sinadarai 46 da kunshe cikin kowanne kwayar halitta (cell). Da zarar guda daya cikin wadannan kwayoyin maniyyi miliyan 75 ya sami damar fasawa, shikenan tamkar ya bada sadaki ta hanyar jarumtarsa. Nan take sai ragowar su saduda su mika wuya. Wato allurar cikin ruwa mai rabo ka dauka. Sum-sum sai duk su janye su baiwa Angon waje ya kama cin angwancinsa.
Maniyyin da ya sami nasara sai su dunkule da kwan, inda zai bada karo-karo na rabin kwayoyin halittar gadonsa, wato 23 inda ita kuma zata bada na ta rabi guda 23. Su na yin wannan karo-karo sai su dunkule su zama kwayar halitta daya (fertilized cell) wanda zai ta shi da cikakkun kwayoyin halittar gado guda 46. To a cikin wadannan kwayoyin halittar gadon (chromosomes) akwai kuma yayansu, wato Genes. Su yayan kwayoyin halittar gado kuma, su ne ke dauke da duk wata siffa ta uwa da uba (da wadda su ka gada da kakanni) irinsu murya, tsawon gashin, jin sanyi ko zafi dss. Wannan auratayya ta maniyyi da Kwan mace sai ya sake hargitsa wadannan kwayoyin halittar gado yadda sabuwar halittar da ta samu sakamakon wannan aure nasu a mahaifa, sai ya samar da sabon mutum (mace ko namiji) wanda ke dauke da kebabbiyar halittarsa ta hanyar gadar kwayoyin halittar uwa da uba.
Allah ya halicci Mani kwaya daya yadda zai iya ajiye bayanai da su ka kai girman Terabyte 160,000 ko mu ce Petabyte 160. Wato misalin abinda kwayar Maniyyi zai iya ajiyewa idan aka kwatanta da computer zai kai fina-finan HD guda miliyan 32, ko mu ce video na HD da zai dauki awanni miliyan 1.6, wato kallo ba kakkautawa na shekaru 182. Ya subhanallah!
Shin mun dauka a banza Allah zai umarce mu da nazarin yadda maniyyi yake? Tsarki ya tabbata ga ubangijin halitta!!!
Malam Ali Sadiq mazaunin Kano ne
