Mu kula da alamomin gargaɗi a yanayin rashin tsaro

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

A daidai lokacin da nake wannan rubutu al’ummar Gundumar Fan dake ƙaramar Hukumar Barikin Ladi a Jihar Filato, na cikin makoki da alhini game da wani harin ta’addanci da aka kai kan wasu masu aikin haƙar ma’adinai, a cikin daren Talatar da ta gabata, inda har aka rawaito cewa an kashe mutane 12 da jikkata wasu mutum biyar da kuma garkuwa da wasu mutum uku. Wannan mummunan al’amari ya daɗa jefa tsoro da firgici a zukatan al’umma da ke wannan yanki, waɗanda sun jima suna fuskantar rashin tsaro da rikice-rikice tsakanin makiyaya da manoma, wanda ake danganta tushen matsalar akan ƙabilanci da addini.

Wannan mummunan al’amari ya faru ne makonni kaɗan da labarin kisan da aka yi wa wasu yara su huɗu a wannan yanki na Gundumar Fan. Bayan ƙorafin da ƙungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta gabatar wa jami’an tsaro da manema labarai, dangane da hare-hare da ake kai wa mutanen su da dabbobin su a ƙauyukan Barikin Ladi da Jos ta Gabas. An rawaito, shugaban reshen ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, yana kokawa da yadda aka sace musu shanu 137 a wani ƙauye dake Barikin Ladi. Sannan an sace wasu shanu 34 a ƙauyen Kukukah dake yankin Jos ta Gabas, kodayake ya ce daga bisani shanu uku sun koma gida da kansu.

Kafin nan akwai rahoton sanya guba a wani waje da shanu ke kiwo a ƙauyen Kwi dake ƙaramar Hukumar Riyom da kuma yankin Gero a Jos ta Kudu, inda nan ma aka rawaito gubar ta kashe shanu 13. Kodayake ƙungiyar matasan Berom waɗanda su ne ƙabila mafi girma a yankin sun ƙaryata zarge-zargen, kamar yadda wani shugaban su Solomon Dalyop ya musanta. Sai dai an daɗe ana ɗora alhakin hare-haren da ake kai wa juna kan masu ɗaukar fansa, cewa da zarar wani abu ya faru a wani ɓangare, ba za a jima ba sai kuma a ji wani abu ya auku a ɗaya sashin. Wannan mummunan al’amari a cewar al’ummar yankin yana ƙara ta’azzara ne, sakamakon hare-haren ta’addanci da suka zargi ƙungiyoyin Fulani masu ɗauke da makamai da kai musu.

Abin takaici ne duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro a yankin suke yi na hana irin wannan hare-hare na ɗaukar fansa abin ya ci tura, ko da kuwa an kai rahoton aukuwar wani abu ga jami’an tsaro, kafin a kai ga kammala bincike ko gano waɗanda suka aikata, sai ka ji wani abu ya sake faruwa a wani gefen. Kai ka ce da gayya ake aikata wani abin, yayin da kowanne ɓangare ke komawa gefe yana nuna yatsa kan ɗan uwansa, da ƙoƙarin wanke kansa. Alhalin ana cigaba da fuskantar asarar rayuka da dukiyoyi, da komabaya a harkokin noma da kasuwanci, musamman kasancewar al’ummar yankunan akasarin su manoma ne da masu aikin ma’adinai.

A cikin wani jawabi da ya gabatar a wajen wani babban taron masu ruwa da tsaki kan yadda za a samar da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka a yaƙi da ayyukan ta’addanci, Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa akwai alaƙa mai ƙarfi tsakanin ayyukan haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, da ayyukan ta’addanci a sassan nahiyar Afirka. Ya kuma danganta hakan da hanyoyin da ýan ta’adda ke samun kuɗaɗe masu nauyi suna sayen manyan makaman da suke haifar da rashin tsaro a ƙasa. Manazarta harkokin tsaro sun daɗe suna tsokaci kan wannan batu da yake ƙara rura wutar ta’addanci a jihohin Arewa maso Yamma, da Arewa ta Tsakiya, kamar su Zamfara, Kaduna da Filato, inda ake ayyukan haƙar ma’adinai da suka haɗa da zinare, kuza, da kwalli, da wasu duwatsu masu daraja. 

Don haka, za a iya danganta harin baya-bayan nan a Jihar Filato kan ƙoƙarin ’yan ta’adda na mamaye wuraren aikin ma’adinai, da tilasta mutanen da suke garkuwa da su yi musu aikin ma’adinan, su tara musu abin da aka samu, don su je su sayar su samu kuɗaɗe masu auki. Zai iya yiwuwa kuma yunƙuri ne na ɗaukar fansa kamar yadda manazarta ke hasashe, biyo bayan ɓarnar da aka yi wa makiyaya na baya-bayan nan a yankin.

Sai dai abin tambaya a nan shi ne, me ya sa masu ruwa da tsaki a yankin ke gaza amfani da dabarun da ake koya musu na amfani da alamomin gargaɗi a matakin farko, a lokacin rashin tsaro, domin ankarar da jami’an tsaro, da kuma ɗaukar matakan rigakafi, da nufin daƙile aukuwar duk wani harin da za a kai na bazata, kan mazauna ƙauyuka cikin duhun dare ko a tsakar rana. Ya kamata a ce bisa la’akari da abubuwan da suke faruwa a wannan yanki cikin waɗannan makonni, da misalin abubuwan da suka faru a baya, a fahimci cewa komai na iya faruwa. Saboda salon faɗan iri ɗaya ne, har yanzu bai canza ba.

A halin da ake ciki, inda rashin kwanciyar hankali da taɓarɓarewar tsaro ke sanya tsoro da fargaba a zukatan jama’a, da hana su barci da iyalansu cikin natsuwa, dole ne mu fahimci muhimmancin amfani da alamomin gargaɗi na matakin farko da ke nuna yiwuwar fuskantar haɗari, ko wani hari da za a iya kai wa ta dalilin aukuwar wani abu. Waɗannan alamomi suna bayyana ne a lokuta daban-daban, kuma idan muka yi nazari da kyau, muka ɗauki mataki cikin sauri, za mu iya guje wa wasu hare-haren da za su salwantar da rayukan jama’a da dama.

A yayin da aka lura da wasu ƙananan abubuwa marasa daɗi na faru nan da can, a kowanne ɓangare. Ko aka lura jita-jita ta fara yawo a kasuwanni da wuraren tarukan jama’a, ko a zaurukan sada zumunta, ana amfani da zafafan kalamai na tunzura juna, ko zarge-zarge marasa tushe to, lallai a yi gaggawar sanar da shugabanni waɗanda su kuma za su sanar da jami’an tsaro, domin ɗaukar matakin da ya dace.

Babu shakka, samar da ingantattun bayanan sirri na taimakawa jami’an tsaro, wajen gaggawar daƙile aukuwar ɓarnar da ba a shirya mata ba. Yana kuma sa a ɗauki matakan da suka dace wajen kai samame maɓoyar ɓatagari a duk inda suke, domin kama su tun kafin su kai ga aiwatar da mummunan nufin su, kuma a samu damar tatsar muhimman bayanai daga wajensu, da nufin ɗaukar matakin doka.

A cewar wani rahoton Majalisar ɗinkin Duniya, ƙasashen dake amfani da tsarin gargaɗi a matakin farko na daƙile aukuwar mummunan al’amari, suna samun nasara kan rage kai hare-hare da kashi 40 cikin ɗari. A Nijeriya, an ƙiyasta cewa samar da ingantattun bayanan sirri sun taimakawa jami’an tsaro wajen saurin ceton rayukan dubban mutane a shekaru 10 da suka gabata. 

Ya zama dole mu zama cikin shiri, mu kasance a ankare, kuma mu yi aiki tare cikin haɗin kai da musayar muhimman bayanai a tsakanin rundunonin jami’an tsaro, da ƙungiyoyin fararen hula masu ba da gudunmawa ta hanyoyin sirri. Alamomin gargaɗi a matakin farko ba hanyoyi ne na cigaba da saka rayukan jama’a cikin haɗari ko fargaba ba, sai don mu kare rayukan juna da al’ummarmu. 

A yayin da muke jajentawa al’ummar Gundumar Fan da jama’ar Filato bakiɗaya, kan wannan babban abin ɓacin rai da ya faru. Muna ƙara kira ga hukumomin da abin ya shafa su daina sanyi da nawa wajen gaggawar ɗaukar mataki da zarar sun samu wani rahoton sirri da suka tabbatar da ingancinsa, domin saurin ɗaukar mataki zai taimaka wajen ceton rai ko da guda ɗaya ne.

Mu ƙara sa ido da lura kan duk abin dake faruwa a inda muke. Mu lura da abubuwan da muke ganin bai kamata a ce sun faru haka ba. Mu amince da jami’an tsaro da hukumomin da muke ƙarƙashin kulawarsu, wajen ba su rahotannin sirri, ba tare da ƙirƙirar ƙarya ko ƙarin gishiri ba. Mu samar da hanyoyi da dabarun tantance da bayanai a tsakanin mu daga ƙauye zuwa birni, da yardar Allah za mu ci nasara akan ‘yan ta’adda da masu hana mu zaman lafiya a garuruwanmu da gidajenmu.

By ukarofi