Za mu tabbatar da ƴancin addini yayin Kirsimeti – Tinubu ga Kiristocin Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga al’ummar Nijeriya da su rungumi zaman lafiya da haɗin kai yayin da Kiristoci ke gudanar da bikin Kirsimeti.

A saƙonsa na Kirsimeti, Tinubu ya ce ƴancin addini muhimmin ginshiƙi ne na ƙasa, yana mai cewa babu wanda ya kamata a tsananta masa ko a cutar da shi saboda aƙida ko addininsa.

Shugaban ƙasar ya sake tabbatar da ƙudurin gwamnatinsa na kare haƙƙin dukkanin ƴan Nijeriya na yin ibada cikin ƴanci da tsaro da kuma kira ga zaman tare cikin lumana da aminci.

“A wannan Rana Mai Tsarki, ina taya dukkan Kiristoci a Nijeriya da ma a fadin duniya murnar Kirsimeti. Ina gode wa Allah da Ya ba ni damar yi wa ƙasarmu mai girma hidima a matsayin shugaba, kuma ina roƙon zaman lafiya a ƙasarmu, musamman a tsakanin mutane masu bambancin addinai”, inji Shugaban.

Tinubu ya kuma yaba wa Kiristoci bisa gudunmawar da suke bayarwa ga cigaban Nijeriya, yana mai yi musu fatan gudanar da bikin Kirsimeti mai albarka da zaman lafiya.

Ya cigaba da cewa: “A matsayina na Shugabanku, ina cigaba da jajircewa wajen yin duk abin da ya dace a ƙarƙashin ikona domin tabbatar da ƴancin addini a Nijeriya da kare dukkan mutane masu mabambantan addinai daga tashin hankali.”

“Yayin da muke bikin haihuwar Yesu, mu kuma yi tunani a kan manyan gudunmawar da Kiristoci a Nijeriya, a matsayinsu na mabiyan Almasihu, suka bayar kuma suke ci gaba da bayarwa wajen ci gaban ƙasarmu”, inji shi.

“Ƙaunar Almasihu da saƙon Bishara sun zaburar da Kiristoci da dama su kula da masu rauni da marasa galihu a cikin al’umma. Muna girmama waɗanda, suna bin misalin Yesu, ke aiki tukuru ba tare da gajiyawa ba domin inganta zaman lafiya, jituwa da haƙuri a cikin al’ummominsu”, kamar yadda ya ƙara.

By Babaji