Daga UMAR GARBA a Katsina
‘Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun yi wa wani jami’in hukumar FRSC kwanton ɓauna a hanyar Funtua zuwa Tafoki da ke ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.
‘Yan bindigar sun kashe Ibrahim Ɗalhatu Tafoki wanda ƙani ne ga ɗan majalisar wakilai a Katsina.
Lamarin ya faru a ranar Talata a dai dai lokacin da marigayin ke tafiya saman babur ɗinsa, inda daga bisani ɓarayin suka gudu da babur ɗin.
An bayyana cewa marigayin ƙani ne ga Rt. Hon. Shehu Ɗalhatu Tafoki, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya a ƙananan hukumomin Ƙankara–Faskari da Sabuwa.
Ya kuma kasance ɗa ne ga Sarkin Tafoki, Alhaji Ɗalhatu Tafoki.
Lamarin ya saka mazauna yankin cikin razani da zaman ɗar ɗar duba da cewa ƙaramar hukumar Faskari na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin jihar Katsina da aka yi sulhu da ‘yan bindiga.
