
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta ya nuna yadda wani gini a garin Offa na Jihar Kwara ya tarwatse sakamakon fashewar wani bom bisa kure.
Hakan ya faru ne sa’o’i bayan Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da cewa sojojinsu sun kai farmaki akan sansanonin ƴan ta’addar ISIS a Jihar Sakkwato.
Mazauna sun tabbatar da cewa sun jiyo ƙararraki bayan wani bom da aka jefo ya faɗi a wani gida, kamar yadda suka shaida a bidiyon.
Saidai a yayin haɗa wannan rahoton, hukumomi ba su tabbatar da ko hakan na da alaƙa da farmakin Sakkwato da Amurka ta kai ba.
A safiyar yau ne gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da haɗin-gwiwar lamuran tsaro tsakaninta da Amurka biyo bayan farmakin na Sakkwato.
A sanarwar da Kakakin Ma’aikatar Harkokin Waje, Kimiebi Ebienfa ya fitar, Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta ce tana cigaba da amfani da hanyoyin diflomasiyya da tsaro tare da abokan hulɗa domin tarwatsa ƴan ta’adda, katse hanyoyin samun kuɗaɗensu da kuma hana su samun sababbin maɓoya gami da ƙarfafa cibiyoyin tsaron gida da kayan leƙen asiri.
