Karamar Hukumar Bichi ta ƙara tallafin kuɗi ga mata masu sana’ar ƙuli

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano ta ƙara tallafin kuɗi ga mata masu sana’ar matsa man ƙuli, domin ƙarfafa su da bunƙasa harkokinsu na kasuwanci.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’ar Yaɗa Labarai ta Karamar Hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta raba wa manema labarai, inda ta ce Shugaban ƙaramar Hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ne ya bayyana hakan yayin da ƙungiyar mata masu sana’ar man ƙuli ta kai masa ziyara a ofishinsa da ke sakatariyar ƙaramar hukumar.

Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana jin daɗinsa bisa yadda ƙungiyar ta nuna amana wajen amfani da tallafin da aka ba su a baya, yana mai cewa wannan shi ne karo na uku da ƙungiyar ke komawa domin neman ƙarin goyon baya.

Alhaji Hamza Sule Mai Fata ya ce gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa mata, musamman a irin wannan sana’a da ke kawo wa jama’a riba, tare da tabbatar da cewa ana samun kasuwa daga wurare daban-daban. Ya bayyana aniyar karamar hukumar na ƙara musu tallafin kuɗi naira dubu dari uku (N300,000) domin ƙarfafa jarin ƙungiyar.

Ya ƙara da cewa, gwamnati na shirye-shiryen fito da wasu tsare-tsare na musamman domin tallafa wa mata, yana mai jaddada cewa duk wanda ya taimaki mace, ya taimaki al’umma gaba ɗaya. Ya kuma tunatar da shirin raba fam da jarin naira dubu hamsin (N50,000) da gwamnatin jihar ke aiwatarwa bisa umarnin mai girma gwamnan Kano.

A nata jawabin, Shugabar ƙungiyar, Malama Hauwa Abdullahi Buden Waje, ta yabawa shugaban ƙaramar hukumar bisa irin goyon bayan da ya riƙa ba su, tana mai cewa a wannan karon sun je ne domin neman tallafin da zai taimaka musu su tsaya da ƙafafunsu, la’akari da ƙwarewar da suka samu har suka kai matakin koyar da wasu.

Haka kuma, Jami’ar Hulɗa da Jama’a ta ƙungiyar, Malama Wali Musa, ta bayyana godiya ga shugaban ƙaramar hukumar da sauran jagororin da suka taka rawa wajen bunƙasa sana’ar, tana mai cewa harkar man ƙuli da gyada na da matuƙar muhimmanci wajen tallafa wa tattalin arzikin yankin Bichi da Jihar Kano gaba ɗaya.

By ukarofi