Tsakanin Aliko Dangote da Farouk Ahmed da yadda rikicin NMDPRA ya ƙazance

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

A cikin makon da ya gabata, Najeriya ta tsinci kanta a tsakiyar wani rikici mai amo wanda ya haɗa fushin jama’a, faɗan manyan masu iko, da kuma damuwar hukumomi.

Rikicin da ya ɓarke tsakanin attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, da tsohon Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta Tsakani da ƙasa (NMDPRA), Injiniya Farouk Ahmed, ya wuce batun mutane biyu kawai, rikici ne da ya shafi makomar gaskiya da amana a harkar mulki, musamman a ɓangaren da ke da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasa.

Shekaru da dama ‘yan Najeriya na kuka da rashin bayyana gaskiya, rashin ɗaukar mataki, da rayuwar alfarma ta wasu jami’an gwamnati wadda ba ta dace da albashinsu ba. Waɗannan koke-koke ne suka samu murya lokacin da Dangote ya fito fili ya zargi Farouk Ahmed da cin hanci da rashawa.

Dangote ya bayyana wannan zargi ne a bainar jama’a, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a matatar man Dangote da ke Lekki, Lagos, inda ya bayyana cewa, Ahmed ya kashe miliyoyin daloli wajen biyan kuɗin karatun ‘ya’yansa a makarantu masu tsada a Switzerland, zargin da ya girgiza zukatan jama’a.

“Akwai wani jami’i da ya kai ‘ya’yansa makarantar sakandare a ƙasashen waje, inda kuɗin karatun shekaru shida na yara huɗu ya kai kusan dala miliyan biyar,” inji Dangote, yana kwatanta hakan da nasa ‘ya’ya da suka yi karatun sakandare a Najeriya.

A cewarsa, batun bai tsaya kan makaranta ba kawai, har da karya yarjejeniyar amana tsakanin gwamnati da masu biyan haraji. Ya jaddada cewa, shi a matsayin sa na babban ɗan kasuwa mai biyan haraji, yana da ‘yancin tambayar yadda ake kashe kuɗin jama’a.

Bayan ‘yan kwanaki, Dangote ya ƙara tsananta rikicin ta hanyar talla ta musamman (adɓertorial) da ya wallafa a manyan jaridu, inda ya lissafa sunayen ‘ya’yan Farouk Ahmed da makarantu masu tsada da ya ce sun yi karatu a cikinsu, ciki har da Institut Le Rosey, Aiglon College, Montreuɗ School, da La Garenne.

Dangote ya ce, irin waɗannan bushasha na dasa alamomin tambayoyi masu nauyi kan bayyana asalin dukiya, yin amfani da muƙami don son kai, da kuma riƙon amana na hukumar da ke kula da man fetur.

A ranar 16 ga Disamba, Dangote ya kai ƙorafi kai tsaye ga Hukumar ICPC, inda ya buƙaci a kama, a bincika, kuma a gurfanar da Farouk Ahmed bisa zargin rayuwa a wajen halal, cin hanci, da karkatar da kuɗaɗen jama’a. Ya kuma bayyana shirinsa na gabatar da hujjoji domin tabbatar da zarginsa.

ICPC ta amsa cikin gaggawa, tana tabbatar da ƙudurin fara bincike, abin da ya nuna girman lamarin da kuma tasirin sunan wanda ya kai ƙarar.

Daga bisani, wata sanarwa da aka danganta da Ahmed ta bayyana a kafafen sada zumunta tana musanta zargin, sai dai daga baya Ahmed ya nesanta kansa da wannan sanarwa, yana cewa ba shi ne ya fitar da ita ba, abin da ya ƙara dagula al’amarin.

Ana cikin haka ne aka sake fitar da bayanin cewa ana zargin Ahmed da shirin amincewa da biyan tsoffin kuɗaɗen “bridging claims” ga ‘yan kasuwa masu hada-hadar mai, lamarin da tuni ke cike da cece-kuce.

A tsakiyar makon, rikicin ya kai ƙololuwa lokacin da Farouk Ahmed ya ajiye muƙaminsa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar da murabus ɗin tare da bayyana cewa, Shugaba Bola Tinubu ya aika sabbin sunaye zuwa Majalisar Dattawa.

Kafin murabus ɗin, Ahmed ya kai ziyara fadar shugaban ƙasa cikin sirri, bai yi magana da ‘yan jarida ba, sannan daga bisani aka sanar da ficewarsa daga ofis.

Majiyoyi sun bayyana cewa, Dangote na ganin wasu matakan da hukumomi ke ɗauka ana amfani da su ne domin hana ko raunana jarin matatar man sa, wanda ya zama ɗaya daga cikin manyan hannun jari masu zaman kansu a Afirka. Har ma an ce ya ɗauki masu bincike na ƙasashen waje domin gano bayanan wasu jami’ai da lamarin ya shafa.

A cewar wani makusancinsa, da ba a tilasta murabus ɗin ba, Dangote na shirin fitar da wasu bayanai da za su iya zubar da mutuncin sunan Farouk Ahmed da iyalinsa matuƙa.

Yayin da ƙura ke lafawa, Najeriya na ƙara zurfafa tambayoyi kan ikon masu kuɗi, amincin hukumomi, da gaskiya a mulki. 

Ko binciken ICPC zai kawo haske ko ƙarin rikici? Lokaci ne kaɗai zai amsa su.

By ukarofi