
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta ce gudu sama da kima da kuskuren kere ne suka yi sanadiyyar hatsarin da ya rutsa da zakara damben duniya, Anthony Joshua.
A jiya Litinin Joshua ya haɗu da iftila’in a kusa da Shagamu, Jihar Ogun, inda abokanansa biyu da suka zo daga Ingila suka rasa rayukansu.
An ga wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta da ke nuna yadda Joshua ya jikkata bayan faruwar al’amarin.
A sanarwar da babban jami’in hulɗa da jama’a da wayar da kai na FRSC, Olusegun Ogungbemide ya fitar, ya ce ba dan dalilai biyun da aka ambata a baya ba, da ba a samu faruwar hatsarin ba.
Ya ce, tuni hukumar ta baza jami’anta domin bada agajin gaggawa ga waɗanda abin ya shafa, wanda ya haɗa motar su Joshua ƙirar Lexus Jeep da wata babbar mota da ta yi jigilar wasu kayayyaki.
Ogungbemide a madadin hukumar, ya miƙa saƙonsu na jaje ga tsohon zakaran damben da kuma iyalan waɗanda suka rasu tare da yi masa fatan samun waraka cikin ƙanƙanin lokaci.
Hukumar ta kuma jaddada gargaɗinta ga masu ababen hawa da su guji yin tuƙin ganganci da kauce wa saɓa wa tsare-tsaren sufuri musamman a manyan titina kamar na Legas zuwa Ibadan.
