Warin baki: Dalilai, rigakafi da magani

Spread the love

Tare da BILKISU YUSUF ALI

Me yake kawo warin baki? 

Warin baki (‘halitosis’ a Turance) na nufin ɗaukar warin da ba daɗi daga cikin baki wanda ke daɗewa ko komawa duk da wankin baki. Ana iya samun warin baki saboda dalilai da dama, waɗanda sun haɗa da:

Rashin tsaftar baki

Wanke baki da goge haƙora sau ɗaya kawai a rana, ko ma rashin goge haƙoran gaba ɗaya. Bakteria (kwayoyin Cuta) su kan taru a tsakanin haƙora da harshe, su fitar da sinadarai masu wari.

Cin abinci mai wari

A kula yayin cin albasa da tafarnuwa da daddawa da sauran abubuwa masu riƙe baki.

Bushewar baki (dry mouth):

Idan bakin mutum ya bushe, yawancin saliva (ruwan baki) da ke wanke cututtuka suna ƙaruwa. Wannan yana bai wa bacteria dama su yi yawa.

Dalilan da suke haifar da bushewar baki 

Shan magunguna kamar  (Antihistamines da  Antidepressants da sauransu) sukan janyo bushewar baki

Rashin shan ruwa akai –akai yana janyo bushewar baki.

Tashin hankali ko rashin kwanciyar hankali ko gajiya (Stress) 

Matsalar harshe:

Bakteria da sauran tarkace suna taruwa a bayan harshe.

Cututtuka.

Ciwon haƙora da ciwon gum (Periodontal Disease) da  ciwon makogwaro da (infection a hanci ko sinuses)

Matsalar ciki (ulcer, acid refluɗ) a wasu lokuta.

Shaye-shaye 

Shan taba da  ganye da  giya da akurkura da sauran kayan maye suna haifar da warin baki. 

Wadannan na da wari su kansu, kuma suna sa bakteria su taru a baki.

Me ya kamata mai warin baki ya yi?

Matakan kulawa da lafiyar baki:

Goge haƙora sau biyu a kowacce rana (safiya da dare) na minti 2–3.

Goge harshe da “tongue scraper” ko brush – musamman bayanin harshe.

Amfani da “mouthwash” da ke da sinadarai kamar chlorheɗidine ko zinc.

Flossing – cire tarkace a tsakanin haƙora.

Shan ruwa sosai – rage bushewar baki.

Rage cin abinci mai wari (tafarnuwa, albasa da sauransu).

Yana da kyau a ziyarci  likitan haƙora aƙalla sau ɗaya a cikin watanni 6 don duba haƙora da dasashi.

Rigakafin warin baki

Abubuwan da za a kiyaye

1. Tsaftar baki a kullum (goge haƙora da goge harshe da  amfani da floss da mouthwash

2. Shan ruwa sosai domin hana baki bushewa

3. Guje wa shan taba da giya da akurkura da sauran abu mai wari da sa maye.

4. Cin abinci mai tsafta da kayan lambu (musamman koren ganye kamar su salad da irin  lemun tsami da parsley da sauran dangoginsu.

5. Ziyarar likita idan kana da ciwon ciki ko ciwon haƙora

Mene ne maganin warin baki me sauƙi? (Magani na gida):

A. Magungunan margajiya (Home remedies):

1. Kurkura baki  da ruwan ɗimi da gishiri yin hakan  yana kashe kwayoyin cuta.

2. Kurkurar baki  da ruwan lemun tsami  da ruwa mai ɗimi. Yin hakan  yana hana bushewar baki.

Cin Koren Ganye kamar:

‘Scent leaf’

Parsley

Na’a-na’a 

Kanumfari 

Basil. 

Waɗannan ganye na da sinadarai masu kawar da warin baki.

Shan lemon tsami ko chewin gum ba tare da sukari ba (sugar-free gum)  shi ma yana sa bakin ya ci ruwa (saliva) sosai.

5. Amfani da baking soda a kurkura baki a ruwan ɗimi  ko a cikin ruwan goge haƙora  yin hakan yana kashe sinadaran wari

 Lokacin da ya Kamata a ga Likita

Idan warin bakin ya fi wata ɗaya yana ci gaba duk da tsaftar, to ya kamata a gaggauta ganin likita.

Idan kana jin zafi a cikin baki ko  makogwaro ko ka gane ka na da matsalar ciki to ya kamata a ga likita.

Idan bakinka yana bushewa sosai fiye da yadda ya kamata shi ma larura ce ya kamata ka ga likita.

Magungunan na zamani:

‘Mouthwash’ mai sinadarin Chlorheɗidine yana kashe bacteria (Misali Corsodyl).

Alburushi masu kariya daga cututtukan ‘bacteria’.

‘Zinc lozenges’ ko ‘mouth sprays’  suna magance wari na baki kai tsaye.

Kammalawa”

Warin baki cuta ce da ke da nasaba da rashin tsafta da nau’in abinci, ko wasu cututtuka. A mafi yawan lokuta, tsafta  da kulawa da baki, mutum na iya kawar da matsalar. Idan warin bakin ya yi tsanani ko ya daɗe to a tuntuɓi  likitan haƙori don a duba domin gano tushen matsalar.

By ukarofi