Borno: Sojoji sun kama ɗan ƙunar baƙin-wake, sun ƙwato sinadaran bom

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun atisayen HAƊIN KAI na rundunar sojin Nijeriya a Jihar Borno, sun yi nasarar cafke wani da ake zargin ɗan ƙunar baƙin-wake ne mai suna Abubakar Mustapha da wasu ababen haɗa boma-bomai.

Kakakin jami’an haɗaka na JTF na rukunin a Arewa ta Gabas, Laftanal Sani Uba ya bayyana haka a wata takarda, ranar Talata.

A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne tun a ranar Litinin a ƙarƙashin jagorancin atisayen runduna ta 152 ta Bataliyar Task Force da haɗin-gwiwar sauran jami’an hukumomin tsaro a Ƙaramar Hukumar Bama da ke arewacin jihar.

Ya bayyana cewa, an yi nasarar haka ne sakamakon samun wasu bayanai na sirri daga yankin Garin Banki na ƙaramar hukumar daga ɓangaren dakarun.

“Da kwatankwacin ƙarfe 5:40 na yammacin Litinin, 29 ga watan Disambar 2025 ne aka baza jami’ai a Babban Masallacin Banki, inda aka kama wani da ake zargin ɗan ƙunar baƙin-wake ne nai suna Abubakar Mustapha”, inji sanarwar.

Laftanal Sani ya ƙara da cewa an kama wanda ake zargin da sinadaran haɗa ababen fashewa na IED da ke nuna ana dab da ƙaddamar da hari.

A halin yanzu ana gudanar da bincike akansa domin ya bayyana masu ɗaukar nauyinsa, waɗanda yake haɗa hannu da su wajen ayyukansa da kuma ƙoƙarin gano hanyoyin da ƴan ta’adda ke bi wajen gudanar da ayyukansu a yankin.

By Babaji