Kaunar talaka da cikakken adalci ne sirrin farin jinin Sarkin Gumel — Umar Danwasha

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugaban ƙungiyar Masarautar Gumel kuma ma’ajin ƙungiyar a Jihar Jigawa, Malam Jafar Umar ɗan Washa, ya bayyana cewa ƙaunar talakawa da cikakken adalci su ne manyan dalilan da suka sa Sarkin Gumel, Alhaji Ahmad Muhammad Sani Mailautai, ke da farin jini da karɓuwa a tsakanin al’ummarsa da ma Nijeriya  baki ɗaya.

Ya ce tun bayan da marigayi tsohon Gwamnan Kano, Alhaji Abubakar Rimi, ya naɗa Sarkin Gumel a shekarar 1985, masarautar ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali, inda bai taɓa jin ƙorafi ko bore daga talakawa ba, sai dai nuna ƙauna da biyayya.

Malam Jafar ɗan Washa ya yi kira ga shugabanni da sarakuna a kowane mataki da su yi koyi da wannan salon shugabanci na adalci da tausayi, domin hakan ne ginshiƙin zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’umma.

Ya kuma jaddada buƙatar al’umma su ci gaba da bayar da haɗin kai, zaman lafiya da addu’o’i ga masarautar Gumel, Jihar Jigawa da ƙasa baki ɗaya.

A ƙarshe, ya ce ƙungiyar Mahauta ta Jigawa za ta ci gaba da haɗa kai da Masarautar Gumel tare da neman shawarwari a ƙarƙashin jagorancin Sarkin Gumel domin bunƙasa ci gaban al’umma.

By ukarofi