Ababen da suka faru a satin bankwana da shekarar 2025 a masana’antun fina-finai na duniya

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

A daidai lokacin da duniya ke bidirin shirye-shiryen karɓar sabuwar shekara, tare da bankwana da shekarar 2025, shafin Taurari ya yi duba da ababen da suka faru a satin ƙarshe na bankwana da shekarar 2025 da zumar taya makaranta masu bibiyar shafin namu murnan sabuwar shekara, tare da fatan Allah Ya sa ta zo mana da tarin alkhairai da kuma silar kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke adabar ƙasarmu.

HOLLYWOOD: Avatar: ‘Fire and Ash’ ya sake girgiza duniya, tare da dawo da mulkin Cameron

Masana’antar shirya fina-finai ta Hollywood ta shiga ƙarshen shekara da gagarumar nasara, yayin da sabon fim ɗin Avatar: Fire and Ash’ ya sake tabbatar da ƙarfin Avatar a kasuwannin duniya. A cikin wannan sati kaɗai, fim ɗin ya zarce dala miliyan 760 a kuɗaɗen shiga, lamarin da ya sa ya mamaye manyan sinimomi a Arewacin Amurka, Turai da wasu sassan Asiya.

Masana harkar fina-finai na cewa, wannan nasara ba ta zo da sauƙi ba, domin a wasu ƙasashe, musamman Indiya, fim ɗin bai kai irin saurin da ‘The Way of Water’ ya yi a baya ba. Duk da haka, abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne yadda Avatar ke ci gaba da zama alamar inganci da jan hankalin masu kallo, shekaru fiye da goma bayan fitowar kashin farko.

“James Cameron ya sake nuna cewa idan aka haɗa labari mai inganci da fasahar zamani, masu kallo ba sa gajiya,” inji wani mai sharhi daga Hollywood Reporter.

BOLLYWOOD: ‘Dhurandhar’ na Ranveer Singh na dab da kafa sabon tarihi a Bollywood

A Indiya kuma, fim ɗin ‘Dhurandhar’ na jarumi Ranveer Singh ya zama abin magana a faɗin duniya. A wannan sati, fim ɗin ya kusanci tara ₹1,100 crore, abin da ya sanya shi cikin jerin fina-finan da suka fi samun kuɗi a tarihin Bollywood.

Duk da tarin nasarorin da fim ɗin ya samu, bai hana shi haɗuwa da ƙalubale ba, domin an hana haska fim ɗin a wasu ƙasashen Gulf, lamarin da ya jawo asarar miliyoyin daloli. Sai dai masu shirya fim ɗin sun bayyana cewa, hakan bai rage musu ƙwarin gwiwa ba, domin kasuwannin Turai, Amurka da Asiya sun ba su goyon baya sosai.

Nasarar ‘Dhurandhar’ ta tilasta wasu manyan fina-finai jinkirta ranakun fitowarsu, domin gujewa fafatawa da shi a kasuwa.

NOLLYWOOD

 ₦512m cikin kwana 12: Funke Akindele ta sake kafa tarihi

Masana’antar Nollywood ta Najeriya ba ta tsaya a baya ba a kammala shekara cikin nasara ba, domin fitacciyar jaruma kuma mai shirya fim, Funke Akindele, ta sake shiga tarihi da fim ɗinta ‘Behind The Scenes’, wanda ya tara sama da ₦512 miliyan cikin kwanaki 12 kacal.

Fim ɗin ya taɓo matsalolin rayuwa na yau da kullum, musamman nauyin da iyalai da al’umma ke ɗora wa mutum, abin da ya sa masu kallo suka ji kamar ana ba su labarinsu ne kai tsaye. Wannan ne ya sa masana ke ganin Nollywood na ƙara komawa kan turbar fim mai zurfin saƙo, ba barkwanci kawai ba, tare da zurfafa tunani kan inganci da nasarar da jarumar ke kawowa a masana’antar. 

Da wannan nasara ne mutane ke tambayar shin Funke Akindele ce ke riƙe da makomar Nollywood a yanzu?

KANNYWOOD

Sabbin fina-finai sun taso: Shin Kannywood ta shirya fita kasuwar duniya?

A Arewacin Najeriya, Kannywood na ci gaba da neman sabon matsayi. A wannan sati, an kammala shirye-shiryen wasu manyan fina-finai da ake sa ran za su fito a farkon sabuwar shekara, inda masu shiryawa ke nuna niyyar shiga kasuwannin Afirka da na ƙetare.

Idan mun yi waiwaye kan shekarar da ta yi bankwana da kuma ta bayan ta, za mu fahinci cewa, shekarar 2025 cike take da cigaba a masana’antar Kannywood, kuma za mu iya kiranta a matsayin shekarar cigaba a masana’antar, duba da irin gagarumar nasara da wasu fina-finai mallakin ta suka samu wanda a tarihin masana’antar ba ta taɓa samun irinta ba.

Zan buga misali da fim mai dogon zango na ‘Labarina’ wanda ya ɗauki tsayin shekaru ana haska shi, duk da haka tagomashin sa sai ƙaruwa yake yi. Da shi kawai idan muka yi mashi dogon nazari za mu fahimci Kannywood ta fara taka matakalan isa inda takwarorinta suka isa.

A ɓangare guda, idan muka kalli fina-finan da aka yi mana alƙawarin fitowar su a wannan sabuwar shekara da irin shirin da aka yi masu, za mu iya hasashen cewa, Kannywood za ta iya kai inda ta jima tana mafarkin tafiya. Hakan kuwa zai tabata ne da taimakon ingantaccen rubutu da labarai masu tsallake iyaka da kuma kayan aiki mafi inganci, sai kuma kwarewar masu sarrafa su.

GHANA WOOD

Ghana Wood na ƙara fitowa fili, fina-finai na shiga kasuwar duniya

Masana’antar fim ta Ghana na ci gaba da samun karɓuwa, musamman a fina-finan soyayya da labaran al’umma. A wannan sati, wasu fina-finan Ghana sun shiga manyan dandamali na kallon fina-finai na duniya (streaming), lamarin da ke nuna cewa Ghawood na samun damar da ba ta taɓa samu ba a baya.

K-ENTERTAINMENT (KOREA)

Damuwa a K-Entertainment: Rikici da rashin lafiyar Ahn Sung-ki na girgiza masoya

Duk da shahararta a duniya, masana’antar K-Entertainment ta Korea ta fuskanci ƙalubale a wannan sati. Rahotanni sun tabbatar da rashin lafiyar fitaccen jarumi Ahn Sung-ki, wanda ya kai shi shiga ICU bayan bugun zuciya, abin da ya jefa masoya damuwa.

A ɓangaren K-pop kuma, rikicin da ya ɓarke a cikin ƙungiyar NewJeans da kamfanin da ke kula da su ya nuna yadda matsin kasuwanci ke ƙara yin tasiri a rayuwar mawaƙa, duk da shahararsu.

Daga ƙarshe, Blueprint Manhaja da ma’aikatanta na yi wa ɗaukacin masoya masu bibiyar ta Barka da Shiga Sabuwar Shekara

By ukarofi