Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Gaggan Turawa waɗanda ke kan gaba cikin wazanda su ka yi wa sassan Amurka mulkin mallaka gabanin kafata a 1776 wato ‘yan Burtaniya, sun miƙa wuya ga Daular Sokoto ta Shehu Usmanu Mujaddadi duk da kwace ikon Daular ta hanyar gwabza yaƙi. Don ganin tsarin shugabanci mai adalci na ilimi da Musulunci mai tsabta, ba bori ba tsafi, sai su ka mulki Daular ta hanyar Sarakuna. Shugaban Amurka na farko da ya jagoranci rundunar juyin juya halin kwatar mulki daga Burtaniya George Washington na da shekaru 22 kacal a duniya a ka haifi Shehu Mujaddadi a 1754. Karankataf tsakanin kafa Amurka daga yankin nahiyar Amurka ta Arewa da Daular Sokoto ta Shehu shekaru 28 ne kacal. Yayin da George Washington ya bar duniya a 1799 ya na mai shekaru 67, Mujaddadi ya bar duniya a 1817 ya na mai shekaru 66. Sai bayan rasuwar Shehu da shekaru 86 a shekara ta 1903 Turwan mulkin mallaka na Burtaniya karkashin Gwamna Lugga wato Frederick Lord Luggard da kwamandan yaƙi Sir Thomas Morland su ka ci Daular Sokoto bayan faro farmaki daga Yola. Masarautar Adamawa na da ƙarfin gaske a Daular Sokoto. Modibbo Adama na daga manyan wakilan Shehu kuma har yau Adamawa na ƙarƙashin jikokin Modibbo ne kazalika da a ka ƙirƙiro jihar daga tsohuwar jihar Gongola sai a ka ɗau sunan Adamawa.
Kai Turawa sun sha mamaki don sun ɗauka za su zo su samu a na taka rawa da waƙa, mata da maza na dabdala, sai su ka yi turus da ganin mutane a natse cikin sutura mai kyau da tsarin karatu da karantarwa ga rangaɗa kiran sallah sau 5 a kullum. Gaskiyar magana tsarinsu na mulkin mallaka bai kama kafar tsarin da su ka tarar na Shehu ba. Shugabanci na tafiya bisa shunfudar addini ga adalci ga kowa. Sun ƙara shan mamaki don Sultan na karshe na Daula Muhammad Attahiru ya ce faufau ba zai zauna karkashin mulkin kafurai ba kuma haka ya ƙi miƙa wuya su ka bi shi har Bormi a yankin jihar Gombe na zamanin yau su ka yi ma sa kisan gilla amma shi ma kwamandan Turawan Manjo Francis Charles Marsh ya sheka barzahu minti 20 kacal bayan harba ma sa wata kibiya daga dakarun Daula. Kabarin Sultan Attahiru da na Manjo Marsh duk na nan a Bormi kuma Turawan Burtaniya na zuwa ziyarar kwamandansu.
Duk Turawan nan sun amfana kwarai da ilimi a aikin da su ka yi na mulkin mallaka a Daular Sakkwato don yanda a ka shimfiɗa tsarin shugabanci na adalci da ba a taɓa gani ba a tsakanin wadannan Daulolin na wannan zamani kuma da alamu har a busa ƙaho ba za a sake kafa Daular da za ta yi tasiri wajen gagarar Bature sauya ma ta salo irin Daular Shehu ba. Kai tsaye zan ce an ci Daular Shehu wajen kwace ragamar iko amma sam ba a ci Daular wajen koyarwa da bin tsarin Musulunci ba. Shehu a shekarun da ya yi a duniya 63 kacal masu albarka amma ya bi koyarwar magabata tun daga tsarin karnonin al’ummar musulunci har zuwa ga Sahabban Manzon Allah mai tsira da aminci. Shehu ya baza ilimi ta hanyar koyarwa da kuma rubuta littattafan ilimi da har yau a ke amfani da su. Kaninsa Malam Abdullahi Gwandu shi ma hamshaƙin malami ne da a ke yi wa taken Balaraben ƙasashen Sudan da zurfin iliminsa da sanin harshen Larabci. Waɗannan bayin Allah sun samu wata baiwa ce daga mahaliccinsu yadda su ka samu zurfin ilimi da kaifin kwakwalwa da hakan ya zama abun mamaki ba sabam ba.
Gaskiyar magana har yau din nan da na ke rubutun nan, Daular Sokoto ta Shehu Mujaddadi na nan kan koyarwar Islama wacce dama asasin kafuwarta kenan don koyar da al’umma sahihiyar akidar musulunci ba shirka, ba bori ba tsafi ba camfe-camfen da ke zama kaucewa hanya.
Allah Maɗaukakin Sarki ya cikawa Shehu burinsa tun ya na raye na ganin al’umma ta hau saiti kan addinin Musulunci don haka Turawa na zuwa su ka miƙa wuya duk da sun zo da addininsu na Kiristanci kuma sun yi marmarin kowa ya zama Kirista.
Zuwa yau shekaru 208 da wafatin Shehu amma KALIMATULLAHI HIYAL ULUYA daga Sokoto har Maiduguri daga Ilori har Yola. To sai kaka kenan ‘yan kwangilar IPOB da sauran maƙiya Arewa?
Kowa ya kwantar da hankalinsa don tabbas ba wani hari da zai wargaza musulunci a yankin Daular Shehu. Addu’o’I da a ka yi dare da rana na aiki a na samun taimakon Allah wajen samun sauki bayan duk wani tsanani.
Kimanin shekaru 57 Turawan mulkin mallaka su ka yi a Arewacin Nijeriya gabanin miƙa mulki ga ‘yan ƙasa a 1960. Sun cimma nasarori da dama ciki da yada harshen turanci, yada addinin Kirista, kawo barasar zamani da zuƙar taba sigari kamar kabusu, haɗa kudanci da arewaci a matsayin kasa zaya a 1914 amma abu ɗaya tak ya gagaresu shi ne sauyawa Musulmi addini zuwa aƙalla dai su zama ‘yan duniya hayaƙin taba, ya zama zuwa masallaci sai Jumma’a ko sallar idi, ya zama Musulunci sai an dawo gida a rabon gado, aure, suna, zakka ko makwabtaka amma in an shiga gari a bi tafarkin Bature. Haka dai Turawa su ka tattara komatsensu su ka koma ba tare da cimma babban muradinsu ba. Wannan na yi wa makiya ciwo musamman gyauron waɗanda su ka bari a baya baƙaƙen Turawa da zuri’arsu da yanzu ke kwangilar yaƙi da Arewa ta hanyar ɗinka rigar ƙabilanci da zummar haddasa yaƙin basasar a yi ta, ta kare a Arewa.
Sultan na ƙarshe mai mulkin Daula wato Sultan na 12 Muhammad Attahiru ya jagoranci mabiyansa su ka fice daga Sokoto da zummar hijira zuwa Madina a kauli mai inganci. Sojojin ‘yan mulkin mallaka su ka bi shi Bormi a jihar Gombe ta yanzu, nan a ka gwabza yaki su ka kashe Sultan da fille kan sa kuma su ka ɗau hotuna su ka rarraba a Arewacin Najeriya don nuna an murƙushe Daular Sokoto. Wannan mataki ya zama mai muni a tarihi duk da an samu wadanda su ka miƙa wuya ga Turawa don gudun kisa.
Sojojin mulkin mallaka sun kashe kusan dukkan jama’ar da ke tare da Sultan Attahiru fiye da mutum 600 ciki da ‘ya’yan Sultan 2 da Limamin Sokoto, amma su ma sun rasa wasu sojojin ciki da kwamandansu Bature Manjo Francis Marsh da ma wasu Turawan da bayanai su ka ƙididdige da 16. A nan a ka bunne Sultan da sauran marigaya. Hakanan shi ma Manjo Francis Marsh. In dangin Sultan da dangin Marsh sun gamu a shekarun baya wajen ziyara a Bormi ba sa kula juna. Rahotanni sun tabbatar da Turawa sun daɗe ba su ziyarci Manjo Marsh ba don haka ciyawa ma ta kange kabarinsa. Ya kamata masoya ‘yan mulkin mallaka su je su nome gewayen kabarin Marsh. Bormi na tazarar kilomita 4 daga garin Bajoga da ke arewacin Gombe kuma kimanin kilomita 76 daga Gombe.
ɗaya daga ‘ya’yan Sultan, Muhammad Bello da a ka yi wa lakabi da Mai Wurno ya jagoranci sauran waɗanda su ka tsira daga kisan Turawa ya isa da su ƙasar Sudan su ka zauna a can. Har yanzu dangin masu hijirar na zaune a Sudan.
KAMMALAWA
Darasin da ke cikin wannan tarihi shi ne da wadanda su ka yi kisan da waɗanda a ka kashe duk ba saura ko mutum daya a raye duk sun koma gidan gaskiya. Sarkin Ingila ma na zamanin King Edward VII ya riga mu gidan gaskiya a fadar Buckingham a 1910. Sarki George V da ya biyo baya ya riga mu gidan gaskiya a 1936. Sai Edward VIII wanda a dalilin nacin wani aure ya rasa sarauta a cikin shekarar da ya hau karaga 1936. Sai Sarki George VI wanda ya hau a 1936 ya riga mu gidan gaskiya a 1952 kuma shi ne mahaifin wacce a ka fi sani a sabon zamanin nan wato Sarauniya Elizabeth wacce ta riga mu gidan gaskiya a 2022 bayan mulkin shekaru 70. Mun san dai yanzu ɗanta Sarki Charles ne ke mulkin fadar Buckingham. Ba mamaki in shi ma rai ya yi halinsa ɗansa Yariman Wales William ya hau karaga. Kaninsa Harry na samun caccaka don rashin auren cikakkiyar Baturiya don haka shi da matarsa Meghan su ka zakuda daga lamuran sarauta su ka koma Amurka da zama.
Gaskiyar magana kowa ya zauna lafiya da juna a guji karɓo kwangilar makiya don tabbas, duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ne ruwan zai doka. Farafagandar ƙabilanci da duk wani sakarci a yi watsi da shi. Wannan zamanin kowa na da ‘yanci a tsarin mulki ya yi addinin da ya ke so ya kuma nemi dukkan muƙamin da ya ke so matukar ya cancanta; amma sam ba a ba wa dan kasa hurumin kulla makirci na tada fitina ba kuma duk wanda ya ƙullawa ƙasa makirci na iya fadawa komar hukuma don fuskantar hukunci kamar yanda ya faru ga madugun ‘yan awaren Biyafara na IPOB Nnamdi Kanu wanda alkali James Omotosho ya yi wa sassauci daga hukuncin kisa zuwa ɗaurin rai da rai. Duk wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho.
