Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wasu sassan birnin Katsina sun faɗa cikin duhu bayan da gobara ta lalata na’urar sauya wutar lantarki (transformer) mai ƙarfin 15MVA a tashar wutar lantarki ta Kofar Ƙaura/IBB Way (Injection Substation).
Gobarar, ta shafi injin TR3 mai ƙarfin 15MVA, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a yankuna da dama na birnin.
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce babu asarar rayuka, sai dai an killace kayan aikin da abin ya shafa domin kare rayuka da dukiyoyi.
Katsewar wutar dai ta shafi Kofar Ƙaura, GRA, Dandagoro, wasu sassan Kofar Marusa; Janbango; Kano Road da makwabtansu, yankuna masu cike da gidaje, kasuwanci, ofisoshin gwamnati da ƙananan masana’antu.
katsewar wutar ta kawo naƙasu ga harkokin kasuwanci, musamman masu sayar da kayan sanyi, da masu sana’ar walda, askin baba, gidajen abinci da cibiyoyin ICT, inda wasu ke cewa ba za su iya dogaro da janareta tsawon rana ba.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na KEDCO, Sani Bala Sani, har yanzu ba a gano musabbabin gobarar ba, amma tawagar fasaha na bincike, tantance asara da kuma maido da wutar lantarki cikin gaggawa.
KEDCO ta ce tsaro da dawo da wuta su ne abubuwan da suka fi ba wa muhimmanci, koda yake ba ta bayyana lokacin da za a dawo da wuta gaba ɗaya ba.
An shiga kwanaki biyu kenan waɗannan wurare da ake ganin cibiyar kasuwanci a garin Katsina basu da wutar lantarki.
