
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar APC reshen Jihar Ribas ta ƙi amince wa da shirin buƙatar tsigewa da Majalisar Dokokin jihar ta fara akan Gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa, Ngozi Odu, inda ta bayyana hakan a matsayin abin da ka iya “haddasa rikici kuma mara muhimmanci”.
A wata wasiƙa da Kakakinta, Darlington ya aike wa manema labarai a ranar Alhamis, APC ta ce tana sane da ikon da dokar ƙasa ta ba ‘yan majalisa amma ba za ta goyi bayan abin da zai kai ga tsige gwamnan da ke ƙarƙashin inuwar APC ba.
Jam’iyyar ta kuma ƙalubalanci mambobinta musamman na majalisar akan taimaka wa matsin lamba ga al’amuran waje da za su iya jefa jihar cikin rikicin siyasa.
Da take warware batun barazanar tsigewar, wadda aka alaƙanta da lamarin kasafi, APC ta tunatar da lokacin mulkin dokar ta-ɓaci da ya gabata a jihar, inda aka miƙa kasafin Naira tiriliyan 1.485 ga majalisar dokokin ƙasa a watan Mayun 2025, wanda Majalisar Dattawa ta amince da shi a 25 ga Yuni, 2025, sai kuma ta wakilai a ranar 22 ga Yuli, 2025.
Acewarta, ana sa ran kasafin zai yi aiki har zuwa watan Agustan 2026.
APC ta bayyana cewa, gwamnan zai iya ƙin gabatar da rarar kasafin, sannan ya tunatar da majalisar cewa doka ta bada damar kashe-kashe na tsawon watanni shida zuwa sabuwar shekarar lissafin kuɗin shiga.
Duk da cewa gwaman bai fitar da wani jawabi akan batun ba, jam’iyyar ta buƙaci majalisar dokokin da ta dakatar da shirin nata, tana mai cewa hakan ka iya janyo wa APC suka da ɓata suna.
