
Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Ƙwararren Lauya Mai Fafutukar neman ‘yancin al’umma, Femi Falana a wata ƙasida, ya gabatar da misalin sakacin shara’a dangane da zargin cin hanci ko rashawa, inda aka zargi wani hafsan hafsoshi yayi ruf-da-ciki da kimanin kuɗaɗe har Naira biliyan 22.8.
Kamar yadda Falana ya zayyana, Babbar Kotun Tarayya Ta Sallame wannan hafsan bisa dalilin wai ba’a ma tuhume shi a Kotun Soji ba, duk da cewar zargin yana da nasaba da zirga-zirga da maƙudan kuɗaɗe.
Babbar Kotun ta sallami hafsan Soji bisa dalilin cewa ita ma Kotun dokar soji (martial court) bata tuhume shi kan zargin laifi da ake tuhumar sa dashi ba, dalilin da hi Falana yake kalubalanta, yana mai cewar laifin da ake tuhumar Hafsan Sojin yana qarwashin hurumin babbar Kotun, ba Kotun dokar soji ba.
Masanin Shara’a Falana yana mai takaicin Wadaqar da kuxaxen jama’a da sunan kuɗaɗen sayen makamai da albarusai, lamarin da yake barin dakarun sojin Najeriya cikin rashin shiri na yaki’, har take kai ga sojojin haya na kasgarar da sojojin Najeriya a fagen fama.
Ya zargi hafsoshin sojin Najeriya da ‘yan kanzagin su farar hula bisa sace biliyoyin kuɗaɗen, ire-iren laifukan suke yin baya ba zani da kotuna har take kaiwa ga sakin masu laifuka ba tare da tuhumar ko bin ba’asi ba
Falana don haka yayi kira na gaggauta samun wata madogarar gwamnati na dawo da dukkan waɗansu kuɗaɗen sayen makamai da aka sace ko karkatar dasu ga ainihin manufar fitowa dasu daga rumbunan tara kuxaxen ‘yan-wasa.
Ya Kuma jaddada cewar, damararrun dakarun sojojin Najeriya dake da wadatattun kayayyakin ayyuka ne suka da kuzarin tsaron qasa da jama’ar ta, ba tare dayin katsalandan daga sojojin qetare ba waɗanda za su haddasa tashin-tashinar addini da zai zama alaƙaƙai wa al’ummar ƙasa.
