Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Manajan Darakta na Hukumar Raya Kogunan Haɗeja–Jama’are (H-JRBDA), Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, ya bayyana cewa dasa bishiyoyi na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da lafiyar muhalli, rage dumamar yanayi da kare ƙasa daga zaizayar ƙasa.
Ya bayyana hakan ne yayin bikin dashen bishiyoyi guda ɗari da aka gudanar a harabar hukumar a Kano, a wani ɓangare na ƙoƙarin yaƙi da dumamar yanayi. Shirin ya gudana ne tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Injiniyoyi mata ta ƙasa, reshen Jihar Kano.
Injiniya Bichi ya jaddada cewa dasa bishiyoyi a wannan lokaci abu ne mai matuƙar muhimmanci, duba da sauyin yanayi da ake fuskanta, inda ruwan sama ke raguwa sakamakon sare bishiyoyi ba tare da maye gurbinsu ba. Ya ce a baya ana samun ruwan sama na tsawon watanni, amma a yanzu hakan ya sauya.
Ya ƙara da cewa baya ga kare muhalli, wasu bishiyoyi na samar da ’ya’yan itatuwa da ke taimakawa wajen inganta lafiyar al’umma. Ya bayyana aniyar hukumar na ci gaba da haɗa gwiwa da ƙungiyoyi masu zaman kansu domin dasa bishiyoyi da kula da su.
Manajan Daraktan ya yaba da gudunmawar ma’aikatan hukumar, ƙungiyoyi masu zaman kansu da shugabannin al’umma wajen wayar da kan jama’a kan amfanin dasa bishiyoyi, tare da yin kira ga masu sare bishiyoyi ba bisa ƙa’ida ba da su guji hakan.
A nata jawabin, Shugabar ƙungiyar Injiniyoyi Mata ta ƙasa reshen Kano, Injiniya Safiyya Aliyu Mahmud, ta ce sun zaɓi haɗa gwiwa da H-JRBDA ne saboda ƙoƙarinta wajen magance matsalar ɗumamar yanayi. Ta ce ƙungiyar ta fara da dasa bishiyoyi guda ɗari, kuma za su ci gaba da shirin a wasu wurare.
Bikin ya samu halartar Manajan Darakta Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, Daraktan Kuɗi da Mulki Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, daraktoci da manyan baƙi.
