Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jam’iyyar ADC na fuskantar sabon gagarumin sauyi a siyasar Nijeriya, bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar, inda aka ce aƙalla ’yan majalisar tarayya takwas na daf da komawa cikinta.
Rahotanni sun nuna cewa Obi, tsohon gwamnan Jihar Anambra, ya kammala shigar sa ADC ne a ranar Laraba a Enugu, inda ya yi kira ga ’yan adawa da ’yan Nijeriya baki ɗaya da su haɗa kai a ƙarƙashin wata babbar haɗaka domin ceto ƙasar daga talauci, rabuwar kai da taɓarɓarewar dimokuraɗiyya.
Da yake bayani kan dalilin barin Labour Party, Obi ya ce matakin da ya ɗauka ya samo asali ne daga kishin ƙasa da muradin al’umma, yana mai jaddada cewa Nijeriya na buƙatar wata sahihiyar madadin siyasa da za ta ƙalubalanci jam’iyyar APC mai mulki.
Obi ya ce, “Wannan mataki na ɗauke shi ne bisa kishin ƙasa da muradin al’umma kawai. Ina kira ga abokan tafiyata na siyasa, Obidient Moɓement da sauran shugabannin adawa a faɗin ƙasar nan da su shigo cikin wannan babbar haɗaka ta ƙasa a ƙarƙashin ADC.” Ya ƙara da cewa, “Tarihi ba zai yafewa shiru ba a lokutan da ƙasa ke fuskantar barazana.”
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na ɗ, Obi ya bayyana cewa akwai ’yan majalisar tarayya masu riƙe da muƙamai da suka halarci bikin shigar sa jam’iyyar, lamarin da ke nuna shirin su na bin sawunsa zuwa ADC.
Daga cikin sanannun sanatocin da ya ambata akwai Enyinnaya Abaribe, ɓictor Umeh, Tony Nwoye da Gilbert Nnaji, tare da fitattun ’yan siyasa da masu tasiri a ra’ayin jama’a.
Majiyoyi daga wurin taron sun shaida cewa an bayyana sunayen ’yan majalisar tarayya takwas da suka amince da komawa ADC gaba ɗaya, ciki har da sanatoci uku da Obi ya ambata.
Ragowar biyar ɗin kuwa ’yan Majalisar Wakilai ne daga Jihar Anambra, wadanda ake cewa sun fice daga Labour Party, sai dai har yanzu ba a sanar da sauyin jam’iyyarsu a hukumance a majalisun tarayya ba, kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Da yake tsokaci kan lamarin, Sakataren Yada Labarai na ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya tabbatar da cewa shigar Obi jam’iyyar ta ƙara mata ƙarfi da jan hankalin ’yan majalisa da dama. Ya ce ADC na sa ran ƙarin fitattun ’yan siyasa da masu riƙe da muƙamai za su shigo jam’iyyar nan ba da jimawa ba, yayin da tattaunawa ke gudana cikin kwarin gwiwa.
A ’yan watannin baya-bayan nan, ADC na gina kanta a matsayin babbar jam’iyyar haɗin gwiwar ’yan adawa, domin tunkarar zaɓen 2027. Jam’iyyar na ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Daɓid Mark, a matsayin Shugaba, yayin da tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola, ke riƙe da muƙamin Sakataren ƙasa.
Tuni dai manyan jiga-jigan siyasa kamar Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Peter Obi suka bayyana aniyarsu ta neman tikitin shugaban ƙasa na ADC a 2027, lamarin da ke nuna cewa fafatawar neman tikitin jam’iyyar na iya zama ɗaya daga cikin mafi zafi a tarihinta.
