Sojoji sun ceto tsohon kanal daga hannun masu garkuwa a Filato

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sojojin Tundunar Sojin ƙasa ta Nijeriya sun samu nasarar ceto wani kanal mai ritaya, Ajanaku, wanda wasu ’yan bindiga suka sace a ƙaramar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato.

Rahotanni sun nuna cewa ceto am sace Kanal ɗin ne a yankin Rafiki, inda dakarun soji daga sassa daban-daban suka kai ɗauki cikin gaggawa bayan samun bayanan satar.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa sojojin sun bi sawun masu garkuwa da mutanen ta hanyar ratsa dajin Wildlife Park, inda aka ƙara ƙaimi wajen bincike da aikin ceto.

An bayyana cewa dakarun sun tsananta bincike a kogo-kogo da kuma manyan duwatsu da ake zargin mafakar masu aikata laifuka ne, matakin da ya sanya masu garkuwa suka fara matsin lamba kan iyalan wanda aka sace.

A cewar wani rahoto daga Zagazola Makama, wata mujalla mai bibiyar harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, masu garkuwar sun tuntuɓi matar Kanal Ajanaku tare da neman kuɗin fansa na Naira miliyan 200, suna barazanar kashe shi idan aka ci gaba da yunƙurin ceto.

Sai dai dakarun tsaro sun sauya dabara zuwa aikin sirri ba tare da hayaniya ba, lamarin da ya kai ga samun nasarar ceto Kanal ɗin da misalin ƙarfe 5:30 na yamma a gefen yankin Rafiki da ke ƙaramar hukumar Bassa. Bayan ceton, an garzaya da shi zuwa wani asibitin soji domin duba lafiyarsa da kuma yi masa cikakken bincike.

Rahoton ya ƙara da cewa, sojojin sun ci gaba da zagaye dazuka da kewaye yankunan da ke kusa, domin cafke sauran ‘yan bindigar da suka tsere bayan ceto mutumin. Ana sa ran bayan an kammala duba lafiyarsa, Kanal Ajanaku zai bayar da muhimman bayanan sirri da za su taimaka wajen ci gaba da farautar masu aikata laifukan.

Mai magana da yawun rundunar soji ta 3rd Diɓision, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce dakarun soji sun ceto tsohon babban jami’in soji cikin nasara. A cewarsa, Kanal ɗin yana samun kulawar lafiya a halin yanzu, kuma za a yi masa cikakken bayani domin tattara bayanan da suka dace.

Tun da fari dai an sace Kanal Ajanaku ne da misalin ƙarfe 12:45 na dare a ranar Litinin daga gidansa da ke kusa da cocin Salɓation Army a titin Rukuba da ke a ƙaramar hukumar Bassa. Lamarin ya tayar da hankulan al’umma kafin samun nasarar ceto shi cikin ƙanƙanin lokaci.

By ukarofi