Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa makomar rayuwarsa ta siyasa za ta shiga mawuyacin hali matuƙa idan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya samu damar yin wa’adi na biyu a zaɓen 2027.
Wike ya ce ba zai sake bari a maimaita abin da ya kira ‘kuskuren siyasa’ na baya ba, yana mai jaddada cewa hakan zai zama tamkar binne kansa ne a fagen siyasa.
An ruwaito cewa Wike ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki na siyasa a ƙaramar Hukumar Okrika ta Jihar Ribas.
A jawabinsa, tsohon gwamnan ya yi magana karara kan makomar siyasar jihar da kuma matsayinsa a zaɓen gwamna mai zuwa.
A cewarsa, tun tuni ɓangarensa na siyasa ya ɗauki matsaya kan zaɓen 2027, musamman dangane da goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma fafatawar kujerar gwamnan Jihar Ribas. Wike ya ce, “Mun riga mun yanke shawara dangane da Tinubu. Amma ɗayan kuma — babu yadda za a yi. Idan muka sake yin kuskure, to mun binne kanmu a siyasa. Ba zan bari a binne ni ba, kuma ba zan sake bari wannan kuskuren ya faru ba.”
Ya ƙara da cewa, shawarar da aka ɗauka ta zama ta ƙarshe, yana mai gargadin masu ruwa da tsaki da su fahimci cewa an riga an kammala zaɓi, ba tare da ja da baya ba.
Maganganun Wike na zuwa ne a daidai lokacin da rikicinsa da Gwamna Fubara ke ƙara tsananta, musamman bayan gwamnan ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a watan da ya gabata. Tun daga wannan lokaci, Wike ya tsananta suka, yana zargin Fubara da karya yarjejeniyar sulhu da aka cimma kafin a dage dokar ta-ɓaci da aka sanya a jihar, wadda ta ba shi damar komawa kan karagar mulki.
A farkon makon nan, Wike ya ce abin da ya kira kuskuren jagoranci da aka yi a Ribas za a gyara shi a 2027, yana mai nuni da cewa zai bayyana cikakkun bayanan yarjejeniyar da ta dawo da Fubara kan mulki idan lokaci ya yi. Ya ce shugabanci ya kamata ya wakilci muradin jama’a, ba burin kai kaɗai ba.
A wata ganawa ta daban da masu ruwa da tsaki a ƙaramar Hukumar Ogba/Egbema/Ndoni, Wike ya yi watsi da ra’ayin cewa goyon bayan Fubara ga Shugaba Tinubu zai ba shi tabbacin sake lashe zaɓe. Ya ce, “Idan ka yi kasuwa da ta farko ka yi nasara, kana ganin za ka yi nasara da ta biyu? Kasuwa biyu ba sa gudana a rana guda.”
Wike ya yi gargaɗi kan duk wani da ke bai wa gwamnan tabbacin cewa komai zai yi kyau muddin ya goyi bayan Tinubu, yana mai cewa hakan kuskure ne babba. Ya jaddada cewa ɓangarensa gaba daya ya yanke shawarar aiki tukuru domin nasarar Shugaba Tinubu, amma hakan ba yana nufin amincewa da tazarce a matakin jiha ba.
Ministan ya kuma zargi Gwamna Fubara da rashin ƙwarewa wajen gina kyakkyawar alaƙa ta siyasa da shugabannin ƙananan hukumomi, ‘yan majalisar jiha da na tarayya. A cewarsa, irin wannan rauni ba zai haifar da shugabanci nagari ba.
Da yake mayar da martani kan kalaman sabuwar shekara na Fubara, inda gwamnan ya kira furucin Wike da “hayaniya”, ministan ya ce ba za a manta da rawar da ya taka wajen kai Fubara kan karagar mulki ba. “Ni ne na mayar da shi gwamna, alhali a wancan lokaci bai da farin jini a wajen jama’a,” inji Wike.
