
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Donald Trump na Amurka ya sake gargaɗin cewa Amurka za ta iya ƙaddamar da hare-hare a Nijeriya a wani karo matuƙar aka cigaba da kisan Kiristoci.
Trump ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da jaridar New York Times da aka wallafa a ranar Alhamis a lokacin da aka masa tambaya akan ko harin farko da ya ƙaddamar a ranar bikin Kirsimeti shi ne mafarin hare-harensa q ƙasar.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da ‘yan siyasar Amurka ke cigaba da ikirarin ana kashe Kiristoci a Nijeriya.
Gwamnatin Nijeriya ta sha musanta ikirarin danganta kashe-kashen ƙasar da kisan Kiristoci kawai.
A cikin hirar da aka yi da Donald Trump, ya ce ya so ya kai hari ɗaya amma idan aka ci gaba da kisan kiristoci, Amurka za ta sake ƙaddamar da wasu hare-hare a ƙasar duk da cewa gwamnatin Nijeriyar ta sha musanta ikirarinda cewa al’amuran ta’addanci sun shafi kowane addini da ƙabila a ƙasar.
