Kano: Ahmad Garba Bichi ya yi alƙawarin tallafa wa ayyukan raya kasuwanci a Bichi

Spread the love

Daga WAKILINMU

Tsohon Ministan Kasuwanci da Masana’antu kuma jagoran Kwankwasiyya a Kano ta Arewa, Alhaji Ahmad Garba Bichi, ya yi alƙawarin bai wa duk wani shiri da ke da nufin haɓaka kasuwanci cikakken goyon baya a ƙaramar Hukumar Bichi.

Alhaji Ahmad Garba Bichi ya bayyana hakan ne yayin da ƙungiyar Kasuwar Zamani ta Bichi ta kai masa ziyarar ban girma a ranar Juma’a, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban kasuwanci da bunƙasar tattalin arzikin yankin.

Tsohon Ministan ya nuna matuƙar farin cikinsa da ziyarar, yana mai yabawa tsarin shugabanci da yadda ake tafiyar da harkokin kasuwar. Ya kuma yi addu’a ga shugabannin kungiyar da ’yan kasuwar baki ɗaya, yana roƙon Allah Ya ba su hikima da ikon sauke nauyin da aka ɗora musu.

Haka zalika, ya yaba wa Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar Hukumar Bichi, Injiniya Dakta Abubakar Kabiru Abubakar Bichi, bisa ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa, musamman waɗanda ke da nufin jawo hankalin ’yan kasuwa daga sassa daban-daban domin zuba jari a yankin.

Alhaji Ahmad Garba Bichi ya kuma yi alƙawarin tuntubar ɗan majalisar tarayyar domin ƙara ƙarfafa ƙoƙarin kammala aikin Kasuwar Zamani ta Bichi, musamman ɓangaren biyan kuɗin gidajen da ake buƙatar saya domin faɗaɗa kasuwar, tare da duba hanyoyin tallafa wa ’yan kasuwa da jarin kasuwanci.

Kazalika, jagoran Kwankwasiyyar ya jaddada aniyarsa ta yin aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙungiyar Kasuwar Zamani domin ganin kasuwar ta kai matsayin da ake buri, tare da yin addu’ar fatan alheri ga kasuwar da ’yan kasuwanta.

Tun da fari, Shugaban ƙungiyar ’Yan Kasuwar Zamani ta Bichi, Alhaji Abubakar Mazahim Saleh, ya bayyana jin daɗinsu bisa kyakkyawar tarba da suka samu daga Alhaji Ahmad Garba Bichi. Ya bayyana ziyarar a matsayin babbar girmamawa, yana mai bayyana shi a matsayin shugaba, jagora, dattijo kuma abin koyi, wanda tarihin yankin ba zai taɓa mantawa da gudunmawar da ya bayar ba, musamman wajen tallafa wa mutane da dama da kuma bunƙasa fannoni daban-daban na rayuwa.

By ukarofi