Idan aka ce mutum ya karya ƙasusuwan jikinsa har guda 90, kai ya bugu fiye da sau 25, sannan kusan kashi 30 cikin 100 na ƙasusuwansa aka maye gurbinsu da ƙarfe da ƙusoshi, da yawa za su ɗauka almara ce ko labarin fim. Amma wannan ba labarin wasan kwaikwayo ba ne. Wannan shi ne ainihin labarin rayuwar Travis Pastrana, hatsabibin ɗan kasada ɗan Amurka wanda ya shahara wajen sayar da ransa domin burge duniya.
Hoton ɗ-ray ɗinsa da ke yawo a kafafen sada zumunta ya gigita mutane. Jiki da ya kamata ya kasance ƙashi da nama, ya koma haɗin ƙarfe da ƙusoshi. Kai ka ce mutum ya gina wani sabon jiki ne bayan tsohon ya gaji. Duk da haka, Pastrana na rayuwa, yana murmushi, yana kuma ci gaba da tsallake abin da yawancin mutane ke kira “iyakar yiwuwa”.
Travis Pastrana ya shahara wajen tsalle-tsalle da babur zuwa sararin samaniya, tsallake dogayen gine-gine, duwatsu da tsaunuka, tare da sauka a wuraren da ba a yi tunanin mutum zai iya tsayawa ba. Sau da dama ya kan faɗo daga jirgi ba tare da lemar sauka ba, yana jingina rayuwarsa kacokan ga ƙwarewa da jarumta. Abubuwan da yake aikatawa ba irin waɗanda ake iya kallo da ido biyu ba ne; dole ne mutum ya rufe ido kafin ya sake buɗewa.
A fagen wasanni, Pastrana ba ƙaramin suna ba ne. Shi ne ɗan wasa mafi yawan lashe kambin zinare a gasar ɗ-Games ta Amurka, gasar da ake kira ‘filin gwajin masu sayar da rai’. Bayan haka, ya yi fice a freestyle motocross, rally racing, NASCAR, Stunt Performance, AMA Motocross da Supercross 125cc, inda ya lashe manyan kambuna sau da dama, abin da ya sanya sunansa cikin tarihin wasannin kasada.
Duk da raunuka da suka taru a jikinsa kamar tarihin yaƙi, Pastrana bai taɓa ɗaukar kansa a matsayin wanda ya gaza ba. A cewarsa, babu wani shamaki da zai hana shi matsawa gaba wajen cimma burinsa, musamman a kan abubuwan da mutane ke ganin ba za su yiwu ba. Wannan ƙudiri ne ya sa ya ci gaba da gwada abin da ya fi ƙarfin jiki, har sai da jikinsa ya koma kamar wani injin da aka gyara sau da dama.
Lokacin da aka tambaye shi adadin raunukan da ya ji tsawon shekarun da ya shafe yana wannan sana’a, amsar tasa ta zama abin mamaki. Ya ce raunukan ba za su irgu ba. Wato ba su da adadi. Wannan kalma guda ta isa ta bayyana irin rayuwar da Pastrana ya zaɓa — rayuwar da ke tsakanin mutuwa da ɗaukaka.
A taƙaice, Travis Pastrana ya zama hujja cewa akwai mutanen da ba sa rayuwa don tsawon lokaci kawai, sai don su bar alama. Kuma idan har akwai wata shaida da ta fi magana kan irin wannan rayuwa, to hoton ɗ-ray ɗinsa ne — hoton da ke nuna yadda mutum ya iya sadaukar da jikinsa gaba zaya domin cika mafarkin da duniya ke kallo da baki buɗe.
