Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jigo a Jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya zargi kwamitin rajistar e-register na membobin APC da ke ci gaba da gudana hana magoya bayansa yin rijista a jihar.
A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa kuma ya bai wa Blueprint Manhaja a Gusau yau Talata, Shinkafi ya ce korar wasu shugabannin ƙananan hukumomi da shugabannin gundumomi daga aikin wani yunƙuri ne na hana magoya bayansa shiga rajistar e-register na membobin jam’iyyar ta APC a jihar.
A cewarsa, reshen APC na jihar Zamfara ya umarci shugabannin ƙananan hukumomi da shugabannin mazaɓu da su cire duk ‘yan APC da ke biyayya gare shi da kuma ‘yan ƙungiyar sa ta siyasa (Wamban Shinkafi Democratic Front).
Dr. Shinkafi ya yi zargin cewa ƙaramin Ministan Tsaro, Hon. Bello Matawalle, shi ne ya shirya kutungwilar hana ‘yan ƙungiyar sa ta siyasa ayi masu rejistar, yana mai cewa magoya bayansa ‘yan jam’iyyar APC ne na gaskiya a jihar Zamfara.
“Akwai jerin ƙorafe-ƙorafe masu yawa daga ‘yan APC waɗanda su ne ‘yan “Wamban Shinkafi Democratic Front” a faɗin ƙananan hukumomi 14 (LGA) da Mazabu 147 a faɗin jihar Zamfara dangane da yadda rijistar Yayan Jam’iyyar APC ke gunana,” in ji shi.
Ya yi kira ga shugaban jam’iyyar na ƙasa da dukkan membobin kwamitin aiki na ƙasa na APC da su magance matsalar korar membobin ƙungiyar siyasarsa, (Wanban Shinkafi Democratic Front).
“IIna roƙon Shugabanmu na Ƙasa na babbar jam’iyyarmu da ya shiga tsakani a kan lamarin don guje wa duk wani yunƙurin rashin haɗin kai da kuma zaman lafiya tsakanin ‘yan jam’iyyar ta APC a Jihar Zamfara”. Shinkafi ya ce.
A cewarsa, waɗanda aka ɗora wa alhakin yin rijistar sun karya dokar da ta tanade su don rashin tabbatar da gaskiyar da shugabannin jam’iyyar na ƙasa suka ba su.
“Akwai buƙatar ɗaukar matakin gaggawa ga shugabannin jam’iyyar na ƙasa domin su tabbatar da cewa akwai gaskiya, adalci da rashin nuna son kai a faɗin ƙasa kan yin rijistar ga tsoffin ‘yan jam’iyyar APC da sabbin ‘yan jam’iyyar a jihar Zamfara, ba tare da la’akari da biyayyar su ga duk wani babban ɗan siyasa ba”.
