Yanzu-yanzu: Super Eagles sun yi adabo da AFCON bayan shan kaye a hannun Moroko

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai masauƙin baƙi, wato Moroko ta tsallake rijiya da baya a yayin da ta doke Nijeriya da ci 4 da 2 a zangon bugun fenareti.

Wannan al’amari ya ba ta damar kaiwa matakin wasan ƙarshe a Gasar Kofin Nahiyar Afirka (AFCON) ta 2025.

An gudanar da wasan ne a Birnin Rabat, wanda ɗan wasa Youssef En-Nesyri ya yi bugun da ya bai wa Moroko nasar akan ‘yan wasan na Super Eagles.

Mai tsaron gida Yassine Bounou ya yi nasarar hana Samuel Chukwueze da Bruno Onyemaechi zura ƙwallo a zangon.

Wannan shi ne karo na farko da mai masauƙin baƙin ta kai wasan ƙarshe tun shekarar 2004, yayin da suke neman sake lashe gasar a karon farko tun 1976.

A yanzu haka dai za ta fafata da Senegal, wadda ta doke Misra da ci 1 mai ban haushi, yayin da ita kuma Nijeriya za ta haɗu Misra a wani wasan don neman gurbi na uku.

By Babaji