Ali Nuhu ya yi albishir ga Kannywood da Nollywood yayin cikarsa shekara biyu a NFC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar 12 ga watan Junairu, 2026 ne Babban Daraktan Hukumar Kula da Finafinan Nijeriya (NFC), Dakta Ali Nuhu ke cika shekaru biyu cif akan muƙamin.

A yayin haka ne ya sanar da cewa, shekarar 2026 za ta samar da sabon salon ci-gaba ga masana’antun Nollywood da Kannywood da ke ayyukansu a Nijeriya da ma ƙasashen ƙetare.

A wani rubutu da Daraktan hulɗa da jama’a na NFC, Brian Etuk ya fitar, Dakta Ali Nuhu ya ce hakan zai taimaka wajen “inganta finafinansu, faɗaɗa hanyoyin rarrabawa a gida Nijeriya da wajenta, sauƙin samun tallafin kuɗi, kayan aiki na zamani, ingantattun cibiyoyi da kuma ƙarin horo ga masu sana’ar fim.”

Ya bayyana cewa, za a cimma haka ne a ƙarƙashin gyare-gyare, haɗin-gwiwa da dabarun aiki da aka aiwatar a shekaru biyu da suka gabata.”ciki har da difulomasiyyar finafinai da ƙasashe kamar Saudiyya, Kanada, Chana, Brazil, Indiya, Iran da Jamaica”, waɗanda aka ƙulla yarjejeniyoyin da su janyo ra’ayoyin masu zuba jari da su da buɗe sabbin kasuwannin harkokin fim.

Ali Nuhu ya ƙara da cewa, sake duba dokar NFC ta 1979 da manufar finafinai ta ƙasa da farfaɗo da shirin National Film Archive da aiwatar da tsarin dabaru na 2025 zuwa 2030 za su kammala a 2026.

By Babaji