Jami’ar Bayero ta yaba wa Hukumar Hadejia Jama’are kan kammala ayyukan samar da ruwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Talata ne tawagar Hukumar Gudanarwar Jami’ar Bayero da ke Kano ta kai ziyayar sada zumunta da godiya a Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are dan nuna jin daɗi da godiya kan kammala ayyukan samar da ruwa a sassan jami’ar.

Shugaban jami’ar, Farfesa Haruna Musa ne ya jagoranci tawagar zuwa ofishin hukumar domin bayyana jinjina da godiya kan kammala ayyukan samar da ruwan bayan tsawon lokaci da jami’ar ta yi na fama da rashin wadataccen ruwa.

Ya ce ayyukan da aka fara tsakanin watan Disamba a shekarar 2025 zuwa watan Janairu 2026 sun taimaka wajen samar da isashen ruwa ga ɗalibai da ma’aikata da al’ummar da ke harkokinsu yau da kullum a jami’ar.

Farfesan ya bayyana cewa cikin ayyukan da aka kammala sun hada da samar da famfunan ruwa masu amfani da solar da gyaran tankunan adana ruwa na karkashin kasa da gyara hanyoyin ruwa dake kai ruwa dakunan kwanan ɗalibai a sabuwa da tsohuwa farfajiyar jam’iar da Goron Dutse da Asibitin Malam Aminu Kano duk da ke ƙarƙashinta.

Yayin jawabin Shugaban Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are, Injiniya Rabiu Suleiman Bichi ya bayyana jindadin da ziyarar da Hukumar Jami’ar Bayero suka kawo wa Hukumar sa. Yace hakan zai karfafa musu gwiwa wajen kokarin cigaba da ayyukan cigaba da Hukumar keyi.

Ya ce, aikin Hukumar ne kula da bunkasa da sarrafa ruwa a Jihohin Kano da Jigawa da Bauchi domin amfani dashi a gidaje da masana’antu da ayyukan noma inda yace jami’ar Bayero na cikin jihohin da Hukumar keda ikon gudanar da ayyukan ta.

Injiniyan ya ƙara da cewa tallafa wa jami’ar da ruwa na muhimmanci saboda kasancewar ta cibiyar bada ilimi da bincike a wannan yankin.

Hon. (Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso Daraktan Kudi da Gudanarwa na Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are da Manyan Daraktocin Hukumar ne suka tarbi manyan baki da suka kawo ziyayar daga jami’ar.

By Babaji