
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen mawaƙin Nijeriya, David Adeleke da aka fi sani da Davido, ya yi tsokaci game da ce-ce-ku-cen Soshiyal Mediya bayan ya rasa Dala 50,000, wato Naira miliyan 50 a sanadiyyar kayen da Super Eagles ta Nijeriya ta sha a hannun Moroko.
A ranar Laraba Moroko ta doke Nijeriya da 4 da 2 a zangon bugun fenariti bayan shafe mintina 120 ana fafatawa a tsakanin ɓangarorin biyu.
Gabanin wasan ne Davido ya sanya zunzurutun kuɗi har miliyan N71 a caca da nufin samun Naira miliyan 495 idan Super Eagles ta yi nasara.
Saidai hakan bai samu a sakamakon rashin nasararsu inda a yanzu suke nema samun matsayi na uku a karawar da za su yi da Misra a ranar Asabar, yayin da Morokon za ta haɗu da Senegal a wasan ƙarshe washe gari.
Bayan kayen ne, Devido, ta kafar Instagram ya ɗora wani hotonsa da ke nuna inda yake cin farfesun kifi gabanin barin Moroko.
Haka kuma an ga ya rubuta “Perfect sign out”, wato fita yadda ta dace.
Wannan al’amari ya janyo ce-ce-ku-ce acikin al’umma musamman bisa la’akari da halin talauci da al’umma ke fama da shi a ce kuma an samu mawaƙi yana ɓanatar da maƙudan kuɗaɗe irin waɗannan ta wasu hanyoyi.
