Gwamnatin Kano ta shirya kai ziyara ƙananan hukumomi 44 don jin ra’ayin al’umma

Spread the love

Daga WAKILINMU

A ƙoƙarin ƙara kusantar gwamnati da al’umma tare da inganta ayyukan jinƙai, Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ayyana ƙudurinta na kai ziyara dukkan ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin jihar domin tattauna matsaloli da damuwar jama’a, tare da lalubo hanyoyin magance su.

Shugaban ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo, ta raba wa manema labarai. Ya yi bayanin ne jim kaɗan bayan ƙaddamar da rabon babura guda 50 da aka bayar kyauta ga jama’ar yankin a sakatariyar ƙaramar hukumar.

Alhaji Hamza Sule Mai Fata ya ce wannan shi ne karo na uku da ƙaramar hukumar ke raba babura kyauta ga waɗanda suka cancanta, ciki har da matasa, magidanta da malamai. Ya ƙara da cewa Gwamnatin Jihar Kano a shirye take wajen tallafa wa al’umma ta fannoni daban-daban na rayuwa.

“Akwai abubuwa da dama da za su zo daga jiha. Mai girma Gwamna yana da niyyar taimaka wa al’umma. Ko jiya an yaye mutum 2,600 da suka rabauta da tallafi iri-iri. Don haka duk wanda bai samu a yau ba, ya yi haƙuri, domin mai yiwuwa gobe shi ne rabonsa,” in ji Alhaji Hamza.

Da yake jawabi, Sakataren ƙokas na yankin, Alhaji Ahmad Haruna, wanda ya wakilci jagoran NNPP na yankin, Alhaji Ahmad Garba Bichi, ya lissafo wasu muhimman ayyuka da Majalisar ƙaramar Hukumar ta aiwatar. Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnati ta tanadi ƙarin shirye-shiryen tallafi, ciki har da bayar da jarin kuɗi ga jama’a.

“Ba za a iya yi wa kowa komai a lokaci guda ba. A hankali ake tafiya, kuma kowa zai samu rabonsa da yardar Allah. Ina kira ga jama’a da su ƙara haƙuri,” in ji Alhaji Ahmad Haruna.

Mutane 50 da suka amfana da kyautar baburan sun nuna matuƙar farin ciki da godiya ga gwamnati. Daya daga cikinsu, Sani Habibu, ya ce ba su taɓa tsammanin za su amfana da tallafin ba, yana mai addu’ar Allah Ya saka wa gwamnati da alheri.

Taron ya samu halartar manyan jami’an ƙaramar hukumar da jiga-jigan siyasa, ciki har da Mataimakin Shugaban ƙaramar Hukumar, Sakataren Mulki, Daraktan Mulki, Shugaban Jam’iyya, Sakataren ƙokas, da sauran manyan baki, inda dukkaninsu suka bayyana goyon baya da fatan alheri ga Gwamnatin Jihar Kano.

By ukarofi