Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta tabbatar da nadin tsohon ɗan wasanta, Michael Carrick, a matsayin koci na riƙon ƙwarya har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana.
Fitaccen masani kan kasuwar ’yan wasa, Fabrizio Romano, ne ya fara bayyana labarin, inda ya ce an kammala yarjejeniyar baki tun ranar Litinin, sannan yanzu an cimma matsaya gaba daya, har da batun tawagar mataimakan da Carrick zai zo da su.
A cewar rahotanni, tsohon ɗan wasan tsakiya na Man United zai zo da wasu amintattun mataimaka, ciki har da wani tsohon ɗan wasan gaba na ƙungiyar, domin taimaka masa wajen jagorantar tawagar.
Romano ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa, “Michael Carrick ya sanya hannu a matsayin sabon koci na riƙon ƙwarya na Manchester United har zuwa ƙarshen kakar wasa. An cimma yarjejeniyar baki tun jiya, yanzu an kammala komai har da batun tawagar koyarwa. Sanarwar hukuma daga kulob ɗin na tafe.”
Carrick ya dawo dandalin horarwa na Old Trafford ne a wani muhimmin lokaci bayan sallamar Ruben Amorim. Shugabannin ƙungiyar na fatan sabon naɗin zai kawo daidaito da kwanciyar hankali, musamman bayan wani lokaci mai cike da ruɗani a cikin gida da kuma filin wasa.
ɗan shekaru 44 din ba bako ba ne a wannan matsayi, domin ya taɓa riƙe muƙamin koci na riƙon kwarya a shekarar 2021 bayan tafiyar Ole Gunnar Solskjaer. A wancan lokacin, Carrick ya jagoranci wasanni uku, inda ya samu nasara sau biyu da canjaras guda, kafin daga bisani ya miƙa ragamar ga Ralf Rangnick.
Carrick na da mutunci da girmamawa sosai a cikin ƙungiyar. Ya shafe tsawon shekaru 12 yana taka leda a Manchester United, inda ya lashe kofuna masu yawa ciki har da Premier League sau biyar, Champions League, FA Cup da kuma Europa League, kafin ya koma fagen koyarwa.
Masu sharhi na ganin cewa kwarewarsa, da kuma cikakken fahimtarsa kan al’ada da burin ƙungiyar, sun taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawarar dawo da shi domin jagorantar tawagar a wannan mawuyacin lokaci.
