
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata Babbar Kotun Ribas da ke zama a Fatakwal, ta haramta wa Alƙalin alƙalan jihar, Mai Shari’a Simeon Chibuzor Amadi, karɓa ko ɗaukar mataki akan kowane saƙon Majalisar Dokokin jihar da ya shafi batun yunƙurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara da Mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu.
Kotun na Ƙaramar Hukumar Oyibo da ke babban birnin jihar ce ta bayar da umarnin bayan gwamnan ya shigar da korafe-korafe guda biyu akan al’amarin.
Akan haka ne kotun ta haramta wa Kakakin majalisar, Martin Amaewhule da wasu mutane 32 ciki har da Akawun majalisar da Alƙalin alƙalan cigaba da yunƙurin tsigewar.
Musamman kotun ta hana babban alƙalin amasr ƙorafin majalisar da ke neman ya yi bincike akan zarge-zargen da suka yi akan gwamnan da suka kai ga neman tsige gwamnan da mataimakiyar tasa.
Mai Shari’a F. A. Fiberesima da ya yi hukunci akan ya sanya takunkumin mutanen aka zayyano ciko har da babban alƙalin.
Daga nan ne ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 23 ga Junairu, 2026.
A makon day a gabata ne majalisar dokokin ta fara shirin tsige gwamnan da mataimakiyarsa, wanda jagoran mafiya rinjayenta, Major Jack ya ƙaddamar bisa abin da ya kira da saɓa wa ƙa’idojin aiki daga ɓangaren jagororin jihar biyu.
