Daga RABIU SANUSI a Kano
Gidauniyar Zuri’ar Sarkin Gini Zakari Ya’u da ke Unguwar cikin ƙaramar Hukumar Birni a Jihar Kano ta tallafa wa mata guda hamsin masu ƙananan sana’o’i da kuɗin jari na Naira dubu hamsin-hamsin, domin ƙarfafa musu gwiwa da kuma basu damar dogaro da kansu.
An gudanar da bikin rabon tallafin ne a wajen taron shekara-shekara na zuri’ar, wanda aka gudanar a dakin taro na motsa jiki na Sani Abacha da ke ƙofar Mata a Kano.
Da yake jawabi a wajen taron, Sarkin Gini na Kano Alhaji Abdulkadir Muhammad Yakasai ya bayyana cewa an shirya taron ne domin kara ɗankon zumunci da haɗin kai a tsakanin ‘ya’yan zuri’ar, tare da taimaka wa mata wajen bunƙasa sana’o’insu.
Ya ƙara da cewa wannan shi ne karo na shida da ake gudanar da taron, inda a kowane lokaci ake bayar da tallafin jari domin taimaka wa mata ‘yan zuri’ar musamman wajen rage dogaro da wasu.
A nasa ɓangaren, ɗaya daga cikin ‘ya’yan zuri’ar, Alhaji Shazali Muhammad Hassan, mai kamfanin HM, wanda Alhaji Ado Muhammad Hassan ya wakilta, ya bayar da tallafin kuɗin jari na Naira miliyan ɗaya domin tallafa wa shirin.
Shi ma Alhaji Kabiru Sani Kwangila ya yi kira ga waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace, domin ci gaban kansu da kuma alherin ƙungiyar baki ɗaya.
Da yake jawabi, shugaban kwamitin shirin, Alhaji Ahmed Shehu, ya bayyana cewa mata 50 ne daga cikin zuri’ar suka amfana da tallafin, domin karfafa sana’o’insu da bunkasa rayuwarsu.
Sauran ‘ya’yan zuri’ar da suka bayar da gudummawa sun haɗa da Alhaji Ibrahim Salisu Gerawa mai kamfanin Gerawa, da Injiniya Abubakar Sadik, wadanda suka bayar da tallafi tare da ƙarfafa gwiwar kwamitin gudanarwa.
Wasu daga cikin matan da suka amfana da shirin, Hajiya Karama Garba Yakasai da Mariya Auwalu, sun bayyana godiyarsu tare da alƙawarin yin amfani da kuɗaɗen ta hanya mafi dacewa.
Taron ya samu halartar manyan baƙi da suka haɗa da Alhaji Abba Yakubu, masu riƙe da muƙamai, da ‘yan kasuwa da dama.
