Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Mai Martaba Sarkin kabin Argungu Alhaji Samaila Muhammad Mera, ya ƙaddamar da kwamitoci a matsayin wani ɓangare na shirye-shirye don samun nasarar bikin kamun kifi da al’adu na Argungu na shekarar daa ke sa ran za a gudanar a watan Fabrairun wannan shekarar ta 2026 (AIF&CF 2026).
Bisa ga al’ada masarautar Kabin Argungu ƙarƙashin jagorancin Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ta kan ƙaddamar da kwamitoci daban-daban na masana daga ɓangarori daban-daban kan al’adun wannan masarautar don shawarwari da kuma gudanar da ayyuka ba tare da samun wata tangarɗa ba a lokacin bikin wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan bukukuwan al’adu na Nijeriya da kuma duniya bakiɗaya.
A lokacin da ya ke jawabi jim kaɗan bayan ƙaddamar da kwamitocin, Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama’ila Muhammad Mera ya umarce su da su samar da cikakkun shawarwari da kamanta kasafin kuɗi na gaskiya cikin ɗan gajeren lokaci bisa ga la’akari da babu isashshen lokaci saboda ana sa ran gudanar da bikin a watan Fabrairu.
A cewar sarkin, an zaɓi membobin a hankali bisa ga tarihin da aka tabbatar, sadaukarwar da suka yi, da kuma gudummawar da suka bayar a baya ga Majalisar Masarautar Argungu, Jihar Kebbi, da kuma ƙasa baki ɗaya.
Ya nuna ƙwarin gwiwa kan iyawarsu ta cika alƙawuran da suka ɗauka da kuma kiyaye al’adun Argungu masu kyau.
Sarkin ya ƙara kira ga dukkan mambobin kwamitin da su yi aiki tare da kiyaye ɗa’a, gaskiya, da jajircewa don tabbatar da samun nasara a wannan bikin na kamun kifi na shekarar 2026.
