An kashe fiye da ‘yan bindiga 200 a Jihar Kogi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Hukumomin Nijeriya sun ce jami’an tsaro sun kashe fiye da ‘yan bindiga 200 a wani “gaggarumin samamen haɗin gwiwa” da aka gudanar a jihar Kogi da ke tsakiyar Nijeriya, yayin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke ci gaba da ƙoƙarin daƙile matsalar rashin tsaro a ƙasar.

‘Yan sanda sun kuma kama wasu da ba a fayyace adadinsu ba, wasu daga cikin su sun ji raunuka daban-daban sakamakon musayar wuta da aka samu. Ana kuma bin sawun sauran ‘yan bindigan da suka tsere, kamar yadda hukumomin suka faɗi.

Kwamishinan harkokin yaɗa labarai na Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya shaida wa Manhaja cewa an lalata sansanonin ‘yan bindiga da dama a lokacin samamen da aka ƙaddamar a ƙarshen mako, wanda ya haɗa da ɓangarori daban-daban na jami’an tsaro da na sojoji.

Ya ce wannan farmaki ya kawo cikas sosai ga ayyukan ƙungiyoyin ‘yan bindiga da ke yankin.

“Har yanzu ana ci gaba da kai samamen, a daren Lahadi an samu musayar wuta mai tsanani a kusa da yankin Obajana, inda jami’an tsaro suka saka ‘yan bindigar cikin mawuyacin hali. Babban matsalar ita ce ‘yan bindigar sun sace mutane da dama suna amfani da su a matsayin garkuwa, domin sun san jami’an tsaro ba za su so su kashe su ba tare da waɗanda suka sace,” inji shi.

Hukumomi sun bayyana cewa an tsara samamen ne tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar da goyon bayan mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da kuma shugabancin hukumomin tsaro na Nijeriya.

Wannan farmakin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Tinubu ke fuskantar matsin lamba daga jama’a wajen daƙile yawaitar tashin hankali a fadin ƙasar, yayin da jihar Kogi ke ƙara zama muhimmin wurin da tsaro ke ƙara taɓarɓarewa saboda hanyar da ke haɗa arewa da kudancin ƙasar ta cikin dazuka.

By ukarofi