Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Dikko Raɗɗa ya yi kira ga zaman Lafiya tsakanin addinai,ya kuma nuna godiya ga Allah maɗaukakin sarki bisa amsa addu’o’in da aka yi domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kuma ƙasa baki ɗaya.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana hakan ne a yayin bikin Mauludin Duniya na Sheikh Ibrahim Inyass na shekarar 2026, wanda aka gudanar a filin wasanni na Muhammadu Dikko da ke Katsina.
Malam Dikko Raɗɗa ya yaba wa masu shirya wannan Mauludi bisa haɗa al’umma cikin yanayi na haɗin kai da ‘yan’uwa.
Ya ƙara da cewa ya dace shugabannin addinai su ci gaba da yin addu’o’i domin cigaba da bunƙasar jihar da ƙasar nan gaba ɗaya.
Haka kuma, Gwamna Radda ya yi kira ga Musulmi da su ci gaba da kasancewa tsintsiya maɗaurin ki ɗaya tare da ƙara haɗin kai da fahimtar juna domin ci gaban al’umma.
Ya gode wa dukkan shugabannin addinin Musulunci da suka halarci Mauludin, tare da yi musu fatan komawa gida lafiya.
A cewar gwamnan, karɓar bakuncin wannan taro na nuna ƙudirin gwamnatin Building Your Future na ƙarfafa zaman lafiya, fahimtar juna da zaman tare cikin mutunci tsakanin addinai.
A nasa jawabin, Khalifa Sheikh Mahi Ibrahim Inyass, wanda Sheikh Muhammadu Kuraish Sheikh Ibrahim Inyass ya wakilta, ya yi kira ga mabiya ɗarikar Tijjaniyya da su rungumi haɗin kai da ‘yan’uwa.
Ya shawarce su da su tafiyar da rayuwarsu bisa koyarwar Alƙur’ani Mai Girma da Hadisan Annabi Muhammadu (SAW) domin gina al’umma nagari.
A nasa ɓangaren, Sarkin Kano na 16, Khalifa Sanusi Lamido Sanusi II, ya yi kira ga haɗin kan al’ummar Musulmi (Umma), tare da roƙon mabiya da su nemi ilimin addinin Musulunci da na zamani (boko), da kuma koyon sana’o’i domin dogaro da kai.
Haka zalika, Khalifan Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, Khalifa Ibrahim Dahiru Usman Bauchi, ya yi kira ga mabiya da su kasance masu bin Alƙur’ani Mai Girma da Hadisan Annabi Muhammadu (SAW), tare da bin koyarwar Sheikh Tijjani da Sheikh Ibrahim Inyass.
Shugaban ƙungiyar a matakin ƙasa, Sheikh Ahmad Tijjani Awwal, ya bayyana cewa mauludin bana na nuna cikar shekaru 40 na Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass a Nijeriya.
Ya yaba wa Gwamna Raɗɗa da kwamitin shirya taron na ƙasa da ƙasa (Local Organising Committee) bisa goyon bayan da suka bayar wajen nasarar gudanar da taron.
Shugaban ƙungiyar a Jihar Katsina kuma Shugaban Kwamitin shirya taron na Jiha, Sheikh Hadi Balarabe, ya nuna godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki bisa gudummawar da suka bayar wajen nasarar Mauludin shekarar 2026.
Taron ya samu halartar manyan mutane da dama da mabiya Ɗarikar Tijjaniyya daga sassa daban-daban na Nijeriya da ma ƙasashen waje.
