Shettima ya jagoranci tawagar Nijeriya a Switzerland don halartar taron tattalin arziƙi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya jagoranci tawagar Nijeriya a taron Tattalin Arziƙin Duniya (WEF) karo na 56 da za a gudanar a Birnin Davos na ƙasar Switzerland.

Za a gudanar da taron ne daga yau 19 zuwa 23 ga watan Junairu, 2026 wanda wakilan ƙasashe da dama za su halarta.

A cewar sanarwar da mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya fitar, Shettima ya samu tarba daga Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar, Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba jari, Dakta Jumoke Oduwole da jami’an jakadancin Nijeriya da ke ƙasar.
‎
‎A taron na bana, Shettima zai gabatar da tsarin tattalin arzikin Nijeriya mai dogon zango, tare da ƙarfafa hulɗa da shugabannin ƙasashe da masu zuba jari.

Haka kuma, taron zai mayar da hankali akan ƙalubalen harkokin tattali a matakin duniya, ƙirƙirarriyar fasaha da sauyin yanayi.

‎Kafin ya isa birnin Sabis, Kashim Shettima ya yada zango a birnin Conakry, ƙasar Guinea ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da Shugaban ƙasar, Mamadi Doumbouya.

By Babaji