Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji biyar sun rasu yayin da ɗan ƙunar-baƙin-waken Boko Haram ya kutsa wa dakaru a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimanin sojoji guda biyar ne suka rasa rayukansu yayin da wasu biyar suka jikkata a lokacin da wani ɗan ƙunar-baƙin-wake ya kutsa cikin tawagar motocin dakarun tsaro a yankin Timbuktu triangle da ke Jihar Borno.

A cewar Daily Trust, majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa al’amarin ya shafi manyan sojoji guda biyu, wato manjo da laftanal.

Sun ce, farmakin ya kuma yi sanadin lalacewar motar yaƙin sojoji da ake amfani da ita wajen kai manyan hare-haren yayin atisaye.

Wata majiya ta ce, ‘yan ta’addar sun yi amfani da wata mota da suka cika ta da ababen fashewa, wadda ta kutsa cikin tawagar sojojin.

Al’amarin ya faru ne a lokacin da sojojin suke dawowa daga wani atisaye da suka samu galaba akan ‘yan ta’adda, inda suka tarwatsa sansanoninsu da halaka da dama daga cikinsu.

Ta ƙarar da cewa, harin ya kuma yi sanadiyyar lalata motocin yaƙi da na makaman sojoji a lokacin da ɗan ƙunar baƙin-waken ya yi katsen a ranar Talata.

Yankin Timbuktu triangle waje ne da ‘yan ta’adda suka yi wa tawagar marigayi Birgediya Janar Musa Uba kwanton ɓauna inda suka kama shi, sannan suka halaka shi daga bisani.

By Babaji