Daga SANUSI MUHAMMAD, Gusau
Gwamnatin tarayya ta nuna gamsuwarta kan ingancin ayyukan tagwayen hanyar da ta tashi daga Zaria zuwa Funtua, Gusau har zuwa Jihar Sokoto.
Ministan ayyuka, Cif David Umahi ya yi wannan tsokaci da yake zantawa da manema labarai a yayin ziyarar gani da ido a ranar Talata, inda ya bayyana cewa an bayar da ayyukan ne a shekarar 2023.
Ministan wanda babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan ayyukan al’umma a Arewa maso Yamma, Abdullahi Tanko Yakasai ya wakilta a lokacin rangadin, ya bayyana cewa za a samar da isasshen tsaro ga dukkan kamfanonin dake gudanar da aiki domin su kammala cikin nasara.
Ya buƙaci kamfanonin Triacta, CGC, Mother Cat da SETRACO da ke kula da aikin da su jajirce wajen inganta aikin.
Ministan Umahi ya yaba wa shugaba Bola Ahmed Tinubu kan damuwar sa na kawo cigaba a Arewa maso Yamma, yana mai cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin kulawar ma’aikatar sa za ta ci gaba da sa ido kan duk ayyukan da gwamnatin tarayya ta bayar don tabbatar da ingantattun ayyuka a ƙasar.
Ya yi gargaɗin cewa duk wani aiki da aka ga bai yi inganci ba, gwamnatin tarayya ba za ta amince da shi ba ta hannun ma’aikatarsa.
Hakazalika, tawagar ministan a lokacin rangadin ta ƙaddamar da titi mai nisan mita 600 da ya haɗa sakatariyar Gwamnatin Tarayya a Gusau da kuma aikin gaggawa a gyaran hanya, yankin Gidan Dawa a Gusau wanda gwamnatin tarayya ta gina.
A cewarsa, titin mai tsawon mita 600 da ya haɗa Sakatariyar Gwamnatin Tarayya a Gusau ya ci gwamnatin tarayya kuɗi har Naira miliyan 641.
Ministan ya nuna godiya ga al’ummomin da ke karɓar baƙuncin Kamfanonin saboda goyon bayan da suke bai wa kamfanonin da ke kula da shi hanyar Zariya-Funtua zuwa Jihar Sokoto wadda ta haɗa jihohin Kaduna, Katsina Zamfara da Sokoto.
